Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja Afrika
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe Afrika
  • Billiri/Balanga: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Sabon Zabe, Amma Gwamnati Ta Yi Shiru – AB Ibrahim Afrika
  • Hukumomin Kashe Gobara A Gombe Sun Ƙarfafa Haɗin Kai Don Hana Gobara A Lokacin Bazara Labarai

Mutfwang Ya Yi Wa Fursunoni 130 Afuwa Yayin Bikin ’Yancin Kan Najeriya
Published: October 1, 2026 at 2:39 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Daga Zainab Babaji a Jos Najeriya

Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya yi wa fursunoni dari da talatin da cikakkiya afuwa a sassan gidajen gyaran hali a jihar yayin da ya mayar da hukuncin kisa na wasu hudu zuwa daurin rai-da-rai.

Gwamnan ya bayyana matakin ahuwar ne a cikin sakon fatan alheri ga ‘yan Najeriya da al’ummar jihar Filato domin murnar cikar kasar shekaru sittin da shida da samun ‘yancin kai.

Sanarwar da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a ga Gwamnan, Gyang Bere ya fitar, ta ce an dauki matakin ne bisa ga ikon da kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya ya bai wa Gwamna, kamar yadda aka yi wa kwaskwarima, sannan kuma bayan tuntubar kwamitin ba da shawara kan ahuwa ta Jiha.

Gwamnan, Caleb Mutfwang a cikin sakon, ya bayyana bikin samun ‘yancin kan a matsayin wata dama ga ‘yan Nijeriya su yi tunani a kan tafiyar kasar tun bayan samun ‘yancin kai, da girmama sadaukarwar da shugabannin da suka kafa ta suka yi, da amincewa da kalubalen da ake fama da su da kuma nuna farin cikinsu da irin nasarorin da kasar ta samu.

Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su sabunta kudurinsu na gina kasa mai dunkulewa, zaman lafiya da wadata, yana mai jaddada cewa gina kasa wani nauyi ne da ya rataya a wuyan jama’a daga wannan zamani zuwa wancan.

A cewar Gwamnan, dole ne a kiyaye hadin kai, diyaucin kasa da kuma iyakokin Najeriya, yayin da ‘yan kasa su tashi tsaye su kawar da bambance-bambancen da ke tsakaninsu, su yi kokarin ganin kasar da kowa ke da ra’ayin zama nasa da kuma damar cimma burinsa.

Mutfwang ya kuma amince da kokarin da shugaba Bola Tinubu ke yi na ganin an dore da hadin kan kasa da zaman lafiya, musamman yadda ya mayar da hankali kan hadin kan kasa, zaman lafiya, da ci gaban tattalin arziki.

Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatinsa na gina jihar Filato inda ‘yan kasa za su iya biyan bukatunsu cikin yanayi na zaman lafiya, tsaro, adalci, da kuma ci gaban kasa baki daya.

Ya yabawa al’ummar jihar Filato bisa juriya da hakuri da kishin kasa, inda ya bukace su da su ci gaba da jajircewa wajen ci gaban jihar da kasa duk da kalubalen da ake fuskanta.

Mutfwang ya taya ’yan Najeriya na gida da na kasashen waje murnar zagayowar ranar, ya kuma yi kira ga ‘yan kasar da su ci gaba da bayar da gudunmawar ci gaban kasa da ta dace da sadaukarwar da jaruman ta suka yi a baya da kuma buri na tsararraki da har yanzu ba a haife su ba.

Ya yi wa ‘yan Nijeriya fatan samun ’yancin kai cikin lumana da ma’ana.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Najeriya @ 66: Tinubu Ya Ce Gwamnati Za Ta Kara Zuba Jari A Noma, Masana’antu Da Bunƙasa Matasa
Next Post: Hukumar Lafiya A Gombe Ta Bukaci Iyaye Su Tallafa Wa Gangamin Rigakafin Tetanus

Karin Labarai Masu Alaka

An Murkushe Wani Yunkurin Juyin Mulki A Jamhuriyar Benin Afrika
Gwamnatin Amurka Na Kokarin Watsi Da Tsohuwar Dokar Jones Labarai
Gwamna Ododo Ya Gargadi Sarakunan Gargajiya Najeriya
Tattalin Arzikin Kasar Congo Ya Bunkasa Labarai
Pasto Yohanna Buru Ya Jagoranci Kiristoci Wajen Bikin Mauludi Tare Da Musulmi A Kaduna Afrika
Fargaba Ta Karu Duk Da Tsagaita Wuta Tsakanin Iran Da Amurka Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Agadez: An Gudanar Da Jana’izar Mutane Da Suka Mutu A Wani Harin Ta’addanci
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja
  • Tambuwal Ya Karyata Rahotannin Shirin Komawarsa APC
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Shugaban Kare Hakkin Dan Adam Na Majalisar Dinkin Duniya Yace RSF Sun Aikata Zalunci Afrika
  • Hukumomin Kasar China Suna Goyon Bayan Somaliya Labarai
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya Afrika
  • Tinubu: Abba Magajin Aminu Kano Ne A Fagen Siyasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NIHSA Ta Yi Gargadin Ambaliyar Ruwa A Jihohi 15 Afrika
  • Shin Ko Ganawar Zelensky Da Macron Zata Haifar Da ‘Da Mai Ido? Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.