Kwamishinan ’Yan Sandan jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chuso, ya tabbatar da cewa rundunar ’yan sandan jihar a shirye take ta ɗauki matakin da ya dace kan duk wani nau’in laifi da munanan ɗabi’u da ka iya kawo barazana ga zaman lafiya da tsaron al’umma.

CP Chuso ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki a bikin Makon Bauta wa Jama’a na ’Yan Sanda na shekarar 2026, wanda aka gudanar a hedikwatar ’yan sandan jihar da ke Gombe.
Taken bikin na bana shi ne “Going the Extra Mile”, wato “Ƙara Ƙoƙari Wajen Bauta wa Jama’a.”
Kwamishinan ya yaba wa al’ummar Jihar Gombe bisa goyon baya da haɗin kan da suke bai wa rundunar ’yan sanda, yana mai cewa haɗin gwiwar al’umma da jami’an tsaro na da matuƙar muhimmanci wajen yaƙi da miyagun laifuka.
Ya ce rundunar za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace kan masu aikata laifuka da sauran abubuwan da ke barazana ga zaman lafiya, tare da tabbatar da cewa jami’an ’yan sanda sun gudanar da ayyukansu cikin ƙwarewa da gaskiya.

CP Chuso ya kuma yi gargadi kan jami’an ’yan sanda, musamman jami’an da ke jagorantar sassan ’yan sanda, da su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Ya ce ba za a lamunci duk wani jami’in da aka samu yana sakaci da aikinsa ko kuma ya kasa ɗaukar matakan da suka dace wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma ba.
Kwamishinan ya buƙaci jama’a da su ci gaba da bai wa ’yan sanda bayanan da za su taimaka wajen dakile aikata laifuka, tare da tabbatar musu da cewa haɗin kansu na da muhimmiyar rawa wajen inganta tsaro.
A nasa ɓangaren, Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Harkokin Gidaje na jihar Gombe, Adamu Dishi Kupto, ya yaba wa jami’an ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro bisa ƙoƙarin da suke yi wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali a jihar.
Ya ce gwamnatin jihar Gombe ta samar da hanyoyin da suka dace domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da tabbatar da ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro.
Sakataren Jama’atu Nasril Islam, JNI, Saleh Danburam, ya tabbatar da cewa JNI da sauran ƙungiyoyin Musulunci za su ci gaba da ba da gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban Jihar Gombe.
Shi ma Wakilin Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Gombe, Mataimakin Daraktan Sashen Tsara Dokoki, David Yohanna, ya bayyana goyon bayan ma’aikatar ga ƙoƙarin ƙarfafa doka da oda da inganta harkokin tsaro.
Shugaban Ƙungiyoyin Fararen Hula, Ibrahim Yusuf, ya yaba wa rundunar ’yan sanda bisa ƙoƙarinta na kare rayuka da dukiyoyi da kuma tabbatar da zaman lafiya.
Shugaban Kwamitin Hulɗa tsakanin ’Yan Sanda da Al’umma, PCRC, na Jihar Gombe, Ubale Garba, ya kuma yaba da buɗe sabon ofishin ’yan sanda na Gwani da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu-Deba.
Sai dai ya yi kira da a yi la’akari da kafa sashen ’yan sanda a Kashere domin ƙara inganta tsaro da kuma kusantar da jami’an tsaro ga al’umma.
A nasa ɓangaren, Shugaban Youth O’Clock a jihar Gombe, Abdulaziz Sani Labaran, ya buƙaci rundunar ’yan sanda da ta sake duba yadda ake amfani da jami’anta wajen yi wa ’yan siyasa rakiya, musamman a lokacin yakin neman zaɓe.
Ya ce yawan tura jami’an ’yan sanda aikin rakiyar ’yan siyasa na iya rage yawan jami’an da ake da su domin gudanar da aikin sintiri da kare sauran jama’a.
Ya kuma bayyana damuwa kan rahotannin kasancewar wasu matasa da ake kira “Kalare” a wasu harkokin siyasa, inda ya ce ana zargin wasu daga cikinsu da ɗauke da makamai.
Ya buƙaci ’yan sanda da su tabbatar da cewa duk wanda aka samu yana ɗauke da makami ba bisa ƙa’ida ba, an ɗauki matakin doka a kansa ba tare da la’akari da alaƙarsa da wata ƙungiyar siyasa ba.
A nasa jawabin, wakilin Babban Hakimin Gombe, kuma Hakimin Gundumar Jalo Waziri, Alhaji Sammani Bappah Yerima, ya yaba wa CP Umar Ahmed Chuso bisa ƙoƙari da jajircewarsa wajen tabbatar da tsaro a jihar.
Ya tabbatar da cewa sarakunan gargajiya za su ci gaba da ba da haɗin kai ga rundunar ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.
Alhaji Sammani Bappah Yerima ya kuma yi kira ga iyaye da su ƙara kula da tarbiyyar ’ya’yansu, domin hana su shiga ayyukan da za su iya kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron al’umma.
Bikin Makon Bauta wa Jama’a na ’Yan Sanda na shekarar 2026 ya kasance wata dama da rundunar ’yan sanda ta yi amfani da ita wajen ƙara ƙarfafa hulɗa da al’umma, tare da tattauna hanyoyin inganta aikin ’yan sanda, gaskiya, riƙon amana da haɗin gwiwa wajen tabbatar da tsaro a jihar Gombe.


