KOTUN BABBAN BIRNIN TARAYYA TA DAWO DON CIGABA DA SHARI’AR TSOHON MINISTA HADI SIRIKA
Babbar kotun birnin tarayya da ke Maitama a Abuja ta dawo zaman cigaba da shari’ar tsohon ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika.
Alkalin kotun Sylvanus Orji na cigaba da sauraron shaidu da bahasin lauyan EFCC Rotimi Jacobs da kalubale daga lauyan sashen kariya Kanu Agabi SAN.
Zaman kotun ya hada da kunna wasu shaidu na faifai inda zuwa yanzu a ka ji tsohon ministan Sirika ya na umurtar a bi ka’idar doka wajen ba da kwangila a ma’aikatar ta sufurin jirage.
A baya dai an kunna wani faifai da a ka dauka a matsayin shaida inda a ka ji Sirika na nuna lallai a dau kwararru ga aikin kafa kamfanin jirage na AIR NIGERIA inda har ya nuna fargabar akwai wasu da ya dace a yi takatsantsan da su.
Hakika an fahimci matakai da dama na ayyukan da a ka gabatar gaban kotun yayin aikin ministan a gwamnatin marigayi shugaba Buhari, sun shafi ayyuka ne kai tsaye da babban sakataren ma’aikatar ya ke da masaniya ko sa hannu a kai.
Za a jira zuwa karshen wannan shari’a da a ke sa ran zai kai ga yanke hukunci bayan kammala dukkan bahasi a karshen watan nan.

Alamu na nuna sashen kariya da Kanu Agabi ke jagoranta na son tsayawa ne kan kariya maimakon tsawaita shari’ar ta hanyar bude shaidun babin kariya.
Hadi Sirika kan halarci zaman kotun kuma ba a samun hayaniya tsakanin lauyoyin EFCC da na kariya fiye da gabatar da shaida da kuma tantance ingancin shaidar.

