Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Afirka Ta Kudu Ta Bukaci Jakadan Israela Ya Fice Daga Kasar
Published: January 30, 2026 at 8:26 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Kasar Afirka ta kudu ta bukaci mataimakin jakadan Isra’ila da ya fice daga kasar cikin sa’o’i 72 ranar Jumu’a, inda ta zarge shi da laifin kassara alakar dake tsakanin kasashen biyu a sakonnin da yake wallafawa a kafafen sada zumunta yana batanci ga shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, abinda ya sabawa ka’idar diplomasiyya.

Ma’aikatar harkokin kasashen waje ta kasar Afrika ta Kudu ta ce zata kori Ariel Seidman na ofishin jakadancin Isra’ila a kasar, kuma bata maraba da shi a kasar ta.

Seidman shi ne jakadan Isra’ila dake da mukami mafi girma a kasar Afirka ta Kudu tun bayan da Isra’ila ta dawo da jakadan ta gida daga kasar a shekarar 2023.

Awanni bayan nan itama Isra’ila ta mai da martani, ta wallafa a shafin ta na X cewa ta kori babban jakadan Afrika ta Kudu, Shaun Edward Byneveldt daga kasar ta, ta kuma umarci shi ya bar kasar cikin sa’o’i 72.

Afrika, Labarai

Post navigation

Previous Post: Tattalin Arzikin Kasar Uganda Zai Bunkasa A Wannan Shekarar
Next Post: Shugaba Donald Trump Ya Nada Shugaban Bankin Tarayya

Karin Labarai Masu Alaka

Kasar Sham Ta Sallami Wasu Fararen Hula Labarai
China Ta Dawo Da Harajin Magungunan Hana Haihuwa Labarai
Mizanin Tattalin Arzikin Najeriya Na 2024 Ya Karu Da Kashi 3.84% Labarai
Kasashen Daular Larabawa Tare Da Saudiya Da Jordan Sunyi Allah Wadai Da kasar Israel Afrika
Ghana Ta Haramta Hakar Ma’adinai A Gandunan Dajin Data Kebe, Labarai
Kasar Masar Ta Dakatar Da Wasu Ayyukan Da Ake Amfani Da Man Fetur Da Diesel Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Duniyar Dambe A Makon Jiya Nishadi
  • Abba Kabir Yusuf Ya Koma Jam’iyar APC Siyasa
  • Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal Ya Bar PDP Ya Koma APC Labarai
  • Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Ya Sauka A Mukaminsa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Birtaniya Ta Bukaci Israela Ta Janye Shawarar Fadada Iko Da Kogin Jordan Labarai
  • Netanyahu: Zamu Kashe Dala Billiyan $110 Cikin Shekaru Hudu Don Kera Makamai Sauran Duniya
  • An Zargi Babban Mai Gabatar Da Kara A Kotun Duniya Ta ICC Afrika
  • Sanyi Mai Tsanani Da Dusar Kankara Ya Tsaida Al’amura A Amurka Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.