Hukumomi a Afirka ta kudu sun fada yau laraba cewa jami’an kasar sun kama ‘yan kasar kenya su bakwai kuma zasu tusa keyar su domin suna aiki ba bisa ka’ida wajen cikewa Amurka takardun bakin haure ‘yan kasar wadanda suke da burin zuwa Amurka da zama.
Jami’an shige da fice na Amukr biyu suna daga cikin wadanda aka kama na wani dan lokaci amma aka sake su, a lokacinda suka gudanar da aikin a jiya talata, kamar yadda wani jami’in hukumar shige da fice na Amurk da wani da yake da masaniya gameda lamarin suka shaidawa kamfanin dillanciin labarai na Reuters, bisa sharadin za’a sakaya sunayen su.
Hukumar shige da fice na Amurka bata maida martani nan da nan ba da aka nemi jin ta bakinta. Sai dai wani jami’in ma’aikatar harkokin wajen Amurka yace Amurka ba zata lamunta da wannan wannan mataki ba. Gwamnatin shugaba Trump tana da burin kwaso farar bata ‘yan Afirka ta kudu zuwa Amurka karkashin wani shiri data fara a shekaran nan, kan zargin cewa ana nuna musu wariyar launin fata. Gwamnatin Afirka ta kudu ta karyata wannan zargi da kakkausar lafazi.


