Afirka ta Kudu ta kubutar da wasu ‘yan kasar su 11 da aka rude su zuwa su taya sojojin Rasha fada a yakin ta da take yi da kasar Ukraine. Ana sa ran mutanen zasu dawo gida nan ba da jimawa ba, a cewar shugan Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa a ranar Talata.
Idan wadannan sun dawo, ya kawo adadin mutanen Afirka ta Kudu da suka dawo gida daga Rasha zuwa 15, bayan da wasu mutane hudu suka iso birnin Johannesburg
Makon da ya gabata bayan da suka shafe watanni suna tafka yaki a sahun gaba a takaddama tsakanin Rasha da Ukrain.
Ana zargin an yaudari mutanen ne da suyi bulaguro zuwa Rasha, da cewar za’a yi musu horo kan harkar tsaro. Shugaba Cyril Ramaphosa ya ce an bi hanyar diplomasiyya ne wajen samarwa da mutanen ‘yancin komawa gida, biyo bayan alkawarin shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a farkon wannan watan


