Yanzu haka dai Al,ummomin da Ambaliyar Ruwan Mokwa a Jihar Nejan Najeriya ta shafa na ci gaba da kokawa akan kasa cika masu alkawalin gina masu wasu gidaje da Gwamnati tayi,
Ambaliyar ta Mokwa da ta faru a damanar bara tayi sanadiyar Asarar daturuwan rayukkan jama,a yayin da wasu mutanen sama da 200 suka rasa gidajensu.
Malam Mohmod Abdullahi Mokwa Yace yanzu haka Akwai daruruwan mutane dake Kwana a filin Allah sannan a sakamakon rashin samar masu da gidajen kamar yadda akayi alkawalin,

Shima Malam Umar Sani Mokwa Wanda yayi bayani a cikin yaren nupanci Yace wadanda suka rasa gidajensu sunfi mutane kuma Alokacin Hukumomin Najeriyar sunyi alkawalin gidaje Amma har yanzu babu Labari,
Yace Idan sunga cewa bazasu iya yi Masu gininba to basu kudadensu su suyi gidajensu da kansu,
To akan wannan Al,amari dai mun tuntubi Kwamishinan Kula da ma,aikatar Jin Kai ta Jihar Nejan Alhaji Ibrahim Inga yace tabbas Akwai korafe korafe daga Mokwa Amma suna kokarin shawo Lamarin,
Ambaliyar ta Mokwa dai ta Samu gagarumar gudunmuwa daga ciki da wajan Najeriya da suka hada da tarin milyoyin Kudi da wasu Gwamnatocin jihohin kasar suka bayar sannan da wau kudi Naira milyan dubu da mataimakin Shugaban kasa Kashim shatima ya bayar a madadin Gwamnatin Najeriyar.

