Sanata Aminu Waziri Tambuwal, tsohon Gwamnan jihar Sokoto kuma Sanata mai wakiltar Mazabar Sokoto ta Kudu, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tare da komawa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
A cikin wata wasika mai kwanan wata 11 ga Maris, 2026 wadda ya aikewa da shugaban jam’iyyar PDP na gundumarsa ta Tambuwal/Shinfiri da ke Karamar Hukumar Tambuwal a jihar Sokoto, Sanata Tambuwal ya bayyana cewa ya ajiye zama dan jam’iyyar PDP nan take.
Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai a Najeriyan ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne bayan zurfin tunani da kuma tuntuba mai fadi da abokan siyasa da magoya bayansa.
A cewarsa, rikice-rikicen cikin gida, sabanin ra’ayi tsakanin shugabannin jam’iyyar da kuma rarrabuwar kawuna da ke ci gaba da addabar PDP sun sa ya zama da wahala a gare shi ya ci gaba da kasancewa a cikinta.
Ya kara da cewa wadannan matsaloli sun raunana hadin kai da kuma alkiblar da jam’iyyar ta tsaya a kai a baya.
Sanata Tambuwal ya kuma nuna godiyarsa ga jam’iyyar PDP bisa damar da ta ba shi ya yi wa kasa hidima a mukamai daban-daban, ciki har da Kakakin Majalisar Wakilai da kuma Gwamnan jihar Sokoto na wa’adi biyu.
Bayan sanar da ficewarsa daga PDP, Sanata Tambuwal ya tabbatar da cewa ya shiga jam’iyyar ADC tare da wasu daga cikin abokan siyasa da magoya bayansa.
Ya bayyana cewa matakin ya samo asali ne daga yakinin da yake da shi na cewa Najeriya na bukatar wata dandalin siyasa mai karfi da za ta ginu kan gaskiya, rikon amana, hada kai da kuma cikakken kudurin bunkasa kasa.
Sanatan ya sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da yi wa Najeriya hidima tare da kare muradun dimokuradiyya, adalci da hadin kan kasa.


