Shugaba Donald Trump na Amurka, ya yarda da shirin tsagaita wuta na tsawon makonni biyu da kasar Iran, ana saura sa’o’i biyu kafin wa’adin da ya ba hukumomin Tehran na su bude mashigin ruwan Hormuz, ko kuma ya sa sojojinsa su kai munanan hare-hare a kan cibiyoyi da kayayyakin bukatu na fararen hular kasar domin aiwatar da abinda ya kira shafe jinsin Farisawa daga doron kasa.
A nata bangaren, Iran ta ce za a fara tattaunawa tsakaninta da Amurka ranar jumma’a a Islamabad, babban birnin Pakistan, kasar da firayim ministanta ya shiga tsakani domin ganin an cimma tsagaita wutar.
Har ya zuwa wannan lokaci, Amurka ba ta tabbatar da yin tattaunawa ido da ido tsakanin kasashen biyu ba, amma ta ce ana tattauna hakan.
Shugaba Trump yace Iran ta gabatar da wasu ka’idoji guda 10 wadanda yace ana iya amfani da su a zaman harsashin yin shawarwari, kuma yana sa ran za a kammala a rattaba hannu a kan yarjejeiya cikin wannan wa’adi na makonni biyu.
Trump yace wannan tsagaita wuta da aka cimma daiai lokacin da aski ke zuwa gaban goshi a wa’ad9n barazanarsa, ta dogara a kan cewa Iran zata kyale a c gaba da jigilar mai ta mashigin ruwan Hormuz.
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya fada cikin wata sanarwar da ya bayar cewa Iran zata dakatar da kai hare-haren ramuwar gayya, kuma zata bari jirage su shige cikin lumana ta mashigin ruwan na Hormuz.
Gidan telebijin na Iran ya ce shugaba Trump ya amince da ka’idojin da Iran ta shimfida na kawo karshen yakin, tana mai bayyana hakan a zaman ba da kai bori ya hau ga shugaban na Amurka.
Kakakin fadar White House Karoline LEavitt ta maida martani da cewa gaskiyar magana ita ce shugaba Trump da karfin sojojin Amurka suka sa Iran ta yarda zata sake bude mashigin ruwan Hormuz, kuma za a ci gaba da tattaunawa.
‘Yan mintoci kadan a bayan da shugaba Trump ya bada sanarwar tsagaita wutar, hannayen jari a Amurka sun cira sama. Farashin man fetur ya subuto kasa, inda a Amurka Farashin gangar danyen mai ya fado da kimanin kashi 17 cikin 100.
Wannan sanarwar tsagaita wuta ta shugaba Trump, sauyin alkibla ce ta mai gaba daya daga abinda ya furta ‘yan sa’o’i kafin nan inda yayi gargadin cewa idan har ba a biya masa bukatunsa ba, to zai shafe jinsin Farisawa daga bangon duniya baki daya cikin daren nan da ya shige.
A halin da ake ciki, jaridar New York Times ta buga rahoton cewa wani jami’in Amurka ya shaida cewa Amurka ta dakatar da duk wani harin sojan da take kaiwa kan kasar Iran bisa sharrudan wannan yarjejeniyar tsagaita wuta ta makonni biyu.
Sai dai kuma a wani bangaren gidan telebijin na Channel 12 na Isra’ila, ya ce sojojin kasar sun kai sabbin hare-hare ta sama kan Iran cikin asubahin larabar nan, a bayan da Trump ya bada sanarwar tsagaita wuta.
Gidan telebijin din yace an kai hare-haren ne a saboda Iran ta ci gaba da harba makamai masu linzami a kan Isra’ila.


