Amurka da jamhuriyar demokuradiyyar kwango suna shawarwari domin kasar ta karbi ‘yan wasu kasashe da Amurka ta tusa keyar su, kamar yadda wasu majiyoyi biyu daga bangaren gwamnati suka gayawa kamfanin dilancin labarai na Reuters a Kinshasa, wadda shine irinsa a baya bayan nan da Amurka ta kulla da wasu kasashen Afirka da dama.
Shawarwarin da wasu majiyoyi uku na MDD, da wasu jami’an difilomasiyya da jami’an Amurka suka yi magana da su, ya nuna yadda gwamnatin Trump take ci gaba da dogaro da wasu kasashe wajen tusa keyar mutane da suka shiga Amurka ba bisa ka’ida ba, ko suka shigo amma suka yi zaman su ba tare da izini ba.
Galibi ana gudanar da wadannan shawarwari ba tare da an daga muriya ba, kuma jama’a basa sanin sharudda da suke kunshe a cikin irin wadan nan yarjejeniyoyi.
Wannan yana zuwa ne a kuma dai dai lokacin da Amurka take kokarin aiwatar yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Kwango da Rwanda, wanda zai baiwa Amurka damar samun ma’adinai daga kasar Kwangon.


