Amurka ta zargi kasar Rwanda da laifin haddasa tashe-tashen hankula da kuma yaki a bayan da ‘yan tawayen kungiyar M23 da take goyon baya a gabashin kasar Kwango ta Kinshasa suka ci gaba da kai hare-hare da kwace yankuna.
Wannan farmaki na ‘yan tawayen na barazanar gurgunta kokarin shugaba Donald Trump na Amurka na kawo zaman lafiya a yankin.
Jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, mike Waltz, ya fadawa Kwamitin Sulhu cewa zasu yi amfani da dukkan karfi da tasirin da suke da shi wajen tabbatar da cewa an hukumta masu gurgunta wanzuwar zaman lafiya.
Hare-haren ‘yan tawayen na baya-bayan nan sun kusanta da wannan fada zuwa bakin iyakar kasar da Burundi, wadda ta yi shekara da shekaru da girka sojojinta a gabashin Kwango bisa gayyatar gwamnatin kasar.
Wannan na kara fargabar cewa wannan rikici da ya janyo mutuwar dubban mutane zai kara yaduwa zuwa wasu sassan yankin.
Waltz ya fada a gaban Kwamitin Sulhun majalisar cewa Amurka tana kira ga Rwanda da ta mutunta alkawarin da ta dauka a karkashin yarjejeniyar da aka cimma, ta kuma mutunta ikon da gwamnatin Kwango take da shi na kare kasarta, da kuma ikonta na gayyatar sojojin kasar Burundi zuwa cikin Kwango domin su taimaka mata wajen kare kasar.


