Amurka ta baiwa Najeriya wasu muhimman kayan yaki, domin taimakawa ayyukan da kasar take yi, kamar yadda rundunar sojin Amurka mai kula da shiyyar Afrika mai lakabin AFRICOM ta fada a yau talata.
Wannan kayayyakin yakin suna zuwa ne bayan da Amurka ta kaddamar da hari da ta auna kan mayakan ISIS a yankin arewa maso yamacin kasar cikin watan jiya.
A cikin bayani data wallafa a dandalin sada zumunci na X, tace kayayyakin da aka mikawa kasar a Abuja, “Zai taimakawa kokarin da Najeriya take yi, wanda ya nuna hadin guiwar kasashen biyu kan batun tsaro.
Sai dai rundunar ta AFRICOM bata bayyana irin kayan aiki da ta baiwa Najeriya ba, wacce take yaki da mayakan sakai masu ikirarin Islama, da kuma galibi kungiyoyin barayin daji daga arewa maso yammacin kasar.


