A bisa rokon hukumomin Najeriya, mayakan Amurka sun kai hare-hare ta sama a kan sansanonin da aka ce na ‘yan kungiyar Daesh, ko ISIS ne, a jihar Sakkwato dake yankin arewa maso yammacin kasar cikin daren nan da ya shige.

Rahoton farko game da wannan harin ya fito ne daga bakin shugaba Donald Trump na Amurka wanda ya ce a bisa umurninsa, Amurka ta kai munanan hare-hare ta sama a kan ‘yan ISIS wadanda a cewarsa su na kashe kiristoci a yankin.

Daga bisani, rundunar sojojin Amurka mai kula da nahiyar Afirka, AFRICOM, ta fito da wata sanarwar dake cewa an kai wannan harin ne bisa rokon hukumomin Najeriya, kuma an kashe ‘yan ISIS da dama.
Ita ma ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, ta fitar da sanarwa dazun nan tana fadin cewa wannan harin da aka kai ya samo asali ne daga yarjejeniyar hadin kan tsaro da musanyar bayanan leke asiri.

Wata sanarwar da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ya bayar cikin daren nan, ta tabbatar da cewa lallai Najeriya ce ta bukaci a kai wannan hari kan sansanonin ‘yan ta’addar a karkashin yarjejeniyar hadin kan tsaron da ta kulla da Amurka da nufin shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Ma’aikatar ta ce gwamnatin Najeriya zata ci gaba da yin aiki da kawayenta ta hanyoyin diflomasiyya da tsaro domin nakkasa ‘yan ta’adda da ayyukansu na ta’addanci a kasar.
A ranar litinin kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ba da labarin ewa tun a cikin watan Nuwamba Amurka ta fara shawagin leken asiri a sassa masu yawa na Najeriya.

Gwamnatin Najeriya ta ce wadannan ‘yan bindiga da kuma ‘yan ta’adda ba su ware addini, suna kai hare-harensu a kan Musulmi da kiruista, kuma ikirarin da Amurka keyi na cewa ana kisan kare dangi ma kirista babu ka mshin gaskiya a cikinsa.

Najeriya ta yarda zata yi aiki da Amurka wajen karfafa yakar wadannan ‘yan ta’adda.


