Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Amurka Ta Kama Tsohon Ministan Kudin Kasar Ghana
Published: January 8, 2026 at 1:16 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Dama dai tun a watan Junairun shekarar da ta gabata ne tsohon ministan kuɗaɗen Ghana, Ken Ofori-Atta ya tsere daga Accra zuwa Amurka da sunan neman lafiya.

Tsohon ministan wanda gwamnatin Accra ta zarge shi da badaƙalar maƙudan kuɗaɗe, har ma ta ce ya tsere daga ƙasar ne saboda gudun fuskantar shari’a, ya nemi tsawaita zamansa a Washington a cewar lauyoyinsa.

To amma jami’an hukumar shige da fice na ƙasar sun kama shi, inda zuwa yanzu babu masaniya game da inda aka ajiye shi a cikin Amurkan.

Sanarwar da tawagar lauyoyinsa suka fitar, ta ce suna tatttaunawa da jami’an tsaron Washington don ganin an sake shi nan bada jimawa ba, a cewarsu shi ma tsohon ministan yana bai wa jami’an haɗin kai.

Ofori-Atta, dai ya kasance ministan kuɗi na Ghana tun daga shekarar 2017 har zuwa ta 2024, zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasar Nana Akufo-Addo, inda ya jagoranci aiwatar da sauye-sauye da dama a fannin tattalin arziƙin ƙasar, wanda gwamnatin John Dramani Mahama ke adawa da su.

Afrika, Amurka

Post navigation

Previous Post: Majalisar Dokokin Rivers Zata Tsige Fubara
Next Post: An tura tsohon ministan Ilimin Nijar gidan yari saboda zargin aikata fyade ga wata daliba.

Karin Labarai Masu Alaka

Masu Kare Hakkin ‘Yan Gudun Hijira A Amurka Sun Mika Koke Amurka
Shugaban Afrika Ta Kudu Yanuna Goyon Bayan Kawo Karshen Yaki Tsakanin Rasha Da Ukraine Afrika
An Gano Kwale-Kwalen Fir’auna A Birnin Masar Afrika
Amurka Zata Fara Sayar Da Maganin Hana Kiba Da Jin Yunwa Amurka
Shugaban Mulkin Soja A Mali Ya Kirkiro Mukami Kamar Minista Afrika
Tsananin Sanyi Ya Kashe Mutane 38 A Amurka Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Kirana Ga ‘Yan Siyasar Arewa, Su Jira Sai 2031- Akume Labarai
  • Kasar Colombia Tare Da Amurka Zasu Fitar Da Man Venezuela Labarai
  • Tinubu: Zamu Kara Kyautata Samar Da Kayan Aiki Ga Jami’an Tsaro Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Bankin Duniya Zaibawa Kasar Mozambique Lamunin Dala Bilyan Shida Labarai
  • Wakilan Majalisar Dokokin Phillipines Suna Yunkurin Tsige Shugaban Kasar Afrika
  • Motar Kungiyar Kwallon Kafar Bayelsa United Ta Yi Hatsari Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Babban Sakataren MDD Yayi Allah Wadai Da Matakin Soja A Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • Janar Christopher Zai Maye Gurbin Ministan Tsaron Najeriya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.