Amurka ta sanya hanu kan sabbin yarjejeniyoyin kan kiwon lafiya da kasashen Madagascar, Saliyo, da Botswana, da kuma Ethiopia, wadda adadin kudaden da shirin zai bukata suka kai kusan dala bilyyan 2 da milyan 300, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fada a ranar talata.
A cikin watan Nuwambana bana ne gwamnatin shugaba Trump ta bayyana wani sabon tsarin tallafi gameda tallafin Amurka take bada wa ga kasashen ketare, da ya fi maida hankali wajen ganin kasashen da take taimakawa suna daukan hakkin kula da kiwon lafiyar kasashen su.
A cikin ko wace yarjejeniya ta kunshi sharudda da suka hada da aiwatar da ita sau da kafa, da kuma matakan ladabtarwa idan aka kaucewa yarjejeniyar, auna ci gaba da ake samu wajen ganin bayan barazana daga wasu cututtuka, da kuma kaucewa dogaro kan tallafin da Amurka take bayarwa, kamar yadda ma’aiktar harkokin wajen Amurka ta fada a cikin wata sanarwa data fitar.
A duka yarjejeniyoyin Amurka ta kuduri anniyar zata kashe kudi dala bilyan daya da milyan dari hudu, yayinda kasashen hudu su kuma za su kashe dala milyan dari tara daga aljehunansu.
Ofishin jakdancin Amurka dake Abidjan babban birnin kasar Ivory Coast ta ce sanya hanu kan yarjejeniyar kiwon lafiya na tsawon shekaru biyar da kasar, za’a gudanar da shi ranar Alhamis idan Allah ya kai mu.
Kamar yadda ofishin jakadancin ya ci gaba da cewa, yarjejeniyar an tsara ta ne da nufin karfafa hanyoyin gano bullar cututtuka da samar da ma’aikata, ta kara da cewa, Amurka zata samarda kudi dala milyan 273, Ivory coast kuma zata bada kudi bilyan 252 na kudin sefa.
Ahalinda ake ciki kuma, matakin janye jakadu masu yawa daga kasashen Afirka da suke kudu da hamadar sahara da Amurka tayi, zai bar Washington bata da manyan kwararru a kusan rabin kasashe da suke yankin, matakin da zai kara dagula yunkurin aiwatar da burin gwamnatin TRump a yankin da yake fama da juyin mulkin soja.
Tun fara aikin gwamnatin Trump, hukumomi a Washington suka bada karfi wajen gudanr da harkokin kasuwanci maimakon bada karfi kan tallafi.
Shugaba Trump ya maida karfi wajen ganin an cimma zaman lafiya, da kuma sanya hanu kan yarjejeniyin samarda muhmman albarkatun kasa, maimakon tallafi.


