Jami’an tsaro a Jamhuriyar Nijar sun dakile wani yunkurin baza kudaden Jabu a harakokin hada hadar kudaden kasar.
Dubban takardun Euro da a ka kyasta cewa darajarsu ta haura milion 600 na CFA ne a ka cafke a hannun wasu matasa a birnin Yamai, lamarin da ya sa al’umma ta jinjinawa jami’an tsaro tare da jan hankulan hukumomi su karfafa matakan tsaro.
Bayanan sirrin da rundunar tsaron Garde Nationale ta bibiya ne suka bai wa dakarunta damar gano wani gida da ke anguwar Nord Lazaret ta birnin Yamai inda ake buga takardun kudade na Jabu.

A yayin samamen da suka kai jami’an tsaro sun kama wasu mutane biyu dukkansu matasan masu kimanin shekaru 30, an same su dauke da dubban takardun kudaden Euro dari biyu-biyu, hade da wasu sinadaran da aka ayyana a matsayin na wankin takardar kudi.
Da ta ke bayyana ra’ayinta kan wannan al’amari Mme Adji Gana Fatouma Souleymane na cewa.
“An kyasta cewa darajar wadanan takardun kudaden Euro na Jabu sun haura milion 600 na CFA wadanda idan aka yi nasarar shigar da su, babbar barzana ce ga tattalin arziki” inji sakataren watsa labaran kungiyar FRSA Salissou Ibrahim.

Buga kudin Jabu na daga jerin miyagun aiyukan da a ka gano cewa suna kokarin samun gindin zama a Nijar, abin da wani mazaunin Yamai Laouali Boubacar yace ya kamata hukumomi su taka musu burki tun da wuri.
Mutanen da rundunar tsaron ta Garde Nationale ta kama ko ba ya ga takardun kudaden Jabu an same su da kakin Soja da tufafin wasannin motsa jiki masu dauke da tambarin ‘yan Sanda.


