Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

An Gano Wani Kurkukun Sirri Da Ake Azaftar Da Mutane A Kasar Libya
Published: January 19, 2026 at 9:08 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumomin tsaron kasar Libya sun kubutar da bakin haure fiye da 200 daga wani kurkukun sirri da aka gina a karkashin kasa a garin Kufra dake yankin kudu maso gabashin kasar, a inda aka tsare su cikin wani mummunan yanayi.

Wasu majiyoyin tsaro biyu a kasar sun ce hukumomi sun gano wannan kurkuku da aka gina mai zurfin mita 3 a karkashin kasa a garin na Kufra wanda wani madugun ‘yan safarar mutane na Libya yake gudanar da shi.

Daya daga cikin majiyoyin yace har yanzu ba a kama mutumin da ya gina yake gudanar da wannan kurkuku na sirri ba.

Majiyar ta ce wasu daga cikin wadannan bakin haure sun shafe shekaru 2 suna daure a ciki. Daya majiyar kuma ta ce sumamen da aka kai ya bankado laifi na cin zarafin bil adama mafi muni da aka taba ganowa a yankin.

Bakin hauren da aka kubutar daga wannan bala’i sun fito ne daga kasashen kudu da hamadar Sahara, kuma akasarinsu daga kasashen Somaliya da Eritrea, kuma sun hada da mata da yara kanana. Garin Kufra yana gabashin Libya, kimanin kilomita 1700 daga Tripoli, babban birnin kasar.

Tun bayan da kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta taimaka wa ‘yan tawaye wajen kawarwa da kashe shugaba Muammar Gaddafi a 2011, Libya ta zamo zangon safarar bakin hauren dake tserewa daga yake-yake da talauci, wadanda ke bi ta wannan hanya mai hatsarin gaske ta cikin hamada bisa zummar samun hanyar kaiwa kasashen Turai.

A makon da ya shige ma, an gano gawarwakin bakin haure su 21 a wani ramin da aka haka aka binne su a yankin na gabashin Libya, inda aka samu wasu da suka kubuta da rayukansu da aka ga alamun an gana musu azaba kafin a sake su

Afrika, Labarai

Post navigation

Previous Post: Wani Jirgin Kasa Yayi Hatsari A Kudancin Spain
Next Post: Shugaba Yoweri Musevini Ya Zamo Shugaban Uganda Na 7 Yana Da Shekaru 81 Kuma Ya Shafe Shekaru 50 A Mulki

Karin Labarai Masu Alaka

Majalisa A Kasar Somaliya Ta Amince Da Sauya Tsarin Mulkin Kasar Afrika
‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Cin Karensu Babu Babbaka A Najeriya Afrika
Iran Zata Mayarwa Amurka Martanin Harin Kharg Afrika
Ministan Harkokin Wajen Iran Yagana Da Shugaban Sa’ido Akan Nukiliya Afrika
Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Samun Sakamako Mai Kyau A Tattaunawa Da Amurka Amurka
Shugaban Kare Hakkin Dan Adam Na Majalisar Dinkin Duniya Yace RSF Sun Aikata Zalunci Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus
  • Hukumar ‘Yan Sanda Sun Dawo Da Dokar Zirga Zirgar Babura A Jihar Gombe
  • Kasar Congo Ta Kawo Karshen Cutar Kyandar Biri
  • Mutane 15 Sun Rasa Rayukan Su A Gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kwango
  • Kungiyoyi Sunyi Kasashen Jinkiri A Bunkasar Tattalin Arzikin Kashen Afirka

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Jirgin Sama Mai Saukar Ungulu Ya Kashe Mutane Biyar A Tanzaniya Afrika
  • Fiye Da Fararen Hula 1000 Yunwa Ta Kashe A Sudan Afrika
  • Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Gombe Ya Ziyarci Pindiga Labarai
  • ECOWAS Da AU Sun Nuna Damuwa Kan Juyin Mulki A Guinea-Bissau Afrika
  • Majalisar Dottawa Ta Kafa Komitin Dokar Zabe Najeriya
  • Dangote Ya Bukaci ICPC Ta Binciki Shugaban NMDPRA Najeriya
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Laraba 11.19.2025 Rediyo
  • Wani Alkali A Amurka Ya Kalubalanci Gwamnatin Kasar Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.