An garkame sojan da ya fi kowane soja a kasar Australiya samun lambobin yabo a gidan kurkuku, a yayin da lauyoyinsa suka kasa neman a yi belinsa bayan da aka kama shi bisa zargin aikata laifuffukan yaki.

Kafofin labarai na Australiya sun ce jiya talata aka kama Ben Roberts-Smith mai shekaru 47 da haihuwa aka tuhume shi da laifuffuka biyar na yaki dangane da kisan wasu fararen hula su 5 tsakanin 2009 da 2012 a kasar Afghanistan.
An ki bada belinsa, inda aka tasa keyarsa zuwa gidan kurkukun ihunka banza na Silverwater dake bangaren yammacin Sydney.


