Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

An Yi Fashin Kaguwa Da Dodon-Kodi Na Miliyoyin Dalar Amurka
Published: December 31, 2025 at 6:50 AM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: December 31, 2025

A wasu al’amura daban-daban da suka faru cikin ‘yan makonni kalilan a yankin arewa maso gabashin Amurka da ake kira New England, barayi sun yi awon gaba da naman kaguwa da dodon kodi guda dubu 40, wadanda aka kiyasta kudinsu ya kai dala dubu 400, kimanin Naira miliyan 581.

Lamarin farko ya faru a garin Falmouth na jihar Maine, inda hukumomi suka ce wani ko wasu sun sace keji 14 cike da dodon kodi daga wata gonar da ake Kiwon su.

Sauran biyun sun faru ne a wani gari mai suna Taunton a Jihar Massachussetts, kimanin kilomita 255 daga inda aka yi na farko, a ranar 2 ga watan nan na Disamba. Sannan a ranar 12 ga watan Disamba, wani direban tirela na bogi yayi shigar burtu yaje aka masa lodin naman kaguwa da aka yi niyyar kaiwa kantunan Costco a jihohin Illinois da Minnessota.

‘Yan sanda suka ce dama an saba satar irin wadannan kayayyakin saboda kudin da ake samu da wajen saida su, amma kuma a ‘yan shekarun nan, abin ya kara yin muni.

Har yanzu babu wanda aka kama dangane da wadannan sace sacen.

Amurka

Post navigation

Previous Post: Jaura Ta Bayyana A Wasu Jihohin Amurka
Next Post: An Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman Don Neman Zaman Lafiya

Karin Labarai Masu Alaka

Dakarun Sojin Amurka Sunfara Sauka A Najeriya Amurka
Masu Kare Hakkin ‘Yan Gudun Hijira A Amurka Sun Mika Koke Amurka
Shirin Kwace Iyakar Greenland Da Shugaba Trump Yakeyi Yabawa Kasashen Turai Mamaki Amurka
A Hudubar Kirsimeti Paparoma Leo Ya Jajantawa Al’ummar Falatsinu A Yankin Zirin Gaza Amurka
Tsananin Sanyi Ya Kashe Mutane 38 A Amurka Amurka
Amurka Tafara Mayar Da ‘Yan Afghanistan Da Suka Makale A Qatar Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Tsohon Minista Ngige Ya Shiga Komar EFCC Najeriya
  • An Gudanar Da Addu’oi Ga Mutane 16 Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe a Australiya Tsaro
  • Kotu Ta Bada Belin Kwamishinan Kudin Jihar Bauchi Najeriya
  • Amurka Ta Kulla Yarjejeniya Da Kasashe Hudu Domin Inganta Kiwon Lafiya Labarai
  • Gwamnatin Amurka Da Najeriya Sunyi Hadakar Inganta Asibiticin Kiristoci Amurka
  • Lauya Bala: Tabbas Kotu Zata Soke Zaben Shugaban PDP, Turaki Najeriya
  • Gobara Ta Lalata Shaguna Da Gidajen Abinci A Gombe Labarai
  • Donald Trump Yace Basu Cimma Matsaya Da Benjamin Natanyahu Ba Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.