‘Yan sandan kasar Australiya sun ce ‘yan bindiga biyu da ake zargin sun kai harin da ya kashe mutane 15 lokacin wani biki na Yahudawa a Bondi Beach dake birnin Sydney, sun yi tattaki zuwa kasar Philippines kafin harin, kuma da alamun masu kaunar akida irinta ISIS ce.
‘Yan sandan sun fada yau talata cewa Sajid Akram mai shekaru 50 wanda kuma aka kashe a wurin, da dansa Naveed Akram, mai shekaru 24 da haihuwa wanda shi ma aka harba amma yana kwance a asibiti, sun tafi kasar Philippines a watan da ya shige, kuma ana bincike abinda ya kai su.
Jami’an kula da shige da ficen baki na Philippines sun ce mutanen biyu sun je Manila babban birnin kasar suka wuce Davao a kudancin kasar daga ranar 1 zuwa ranar 28 ga watan Nuwamba da suka baro can, makonni kadan klafin harbe-harben na Bondi.
Uban ya je shi Philippines dauke da Fasfo na kasar Indiya, shi kuma dan da fasfo na Australiya.
Hukumomi suka ce babu wata shaida da ta nuna wata alaka a tsakaninsu da wata kungiyar ta’addanci ko kuma sa mun horo daga ire-iren su.
Wani musulmi magidanci mai suna Ahmed al Ahmed da ake yaba masa a zaman gwarzo a bayan da yayi kukan kura ya abka kan daya daga cikin ‘yan bindigar, sannan yana kwance a asibiti a Sydney yana jinyar harbinsa da aka yi har sau hudu.
Shugabannin Australiya da ma shugaba Donald Trump na Amurka suna yaba ma Ahmed a zaman gwarzo.
Asusun da aka kafa na nema masa gudumawar kudin jinya a yanzu ya tara fiye da Dala miliyan 1 da dubu 260.


