Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana aniyarta ta sake ƙarfafa dakarun tsaron ƙasar, domin tunkarar matsalolin tsaro da ke addabar wasu sassa.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya bayyana hakan a yayin taron addu’o’i na musamman da aka shirya domin dakarun tsaron ƙasa a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja.

Shettima ya yaba da jajircewa da sadaukarwar da dakarun tsaron ƙasar ke yi, musamman waɗanda suka rasa rayukansu a bakin aiki wajen kare martaba da ikon ƙasar, da kuma rayuka da dukiyoyin al’umma.
Taron addu’o’in ya gudana ne a matsayin wani ɓangare na bukukuwan ranar tunawa da gudunmowar da dakarun tsaron Najeriya ke bai wa ƙasa.

Gwamnatin Tarayya ta ware ranar 15 ga watan Janairu na kowace shekara domin karrama dakarun tsaron ƙasar.


