Britaniya ta tura dakarunta na ruwa domin hana jiragen ruwan Rasha masu tafiya karkashin ruwa yanke woyoyi da bututu-bututu da suke karkashin ruwa, Ingila tace jirgen ruwan na Rasha sun zauna a ruwayen da suke ciki da kewayen Ingila fiye da wata daya a farkon shekaran nan, kamar yadda ministan tsaron kasar John Healey ya fada jiya Alhamis.
Britaniya ta zargi Rasha da fakewa da rikicin gabas ta tsakiya domin ta gudanar da miyagun ayyuka a hanyoyin ruwa da suke yankin.
Healey yace dakarun Ingila da na kewaye da suka hada da Norway, sun bi jiragen ruwan na Rasha domin hana su yin barna, ya kara da cewa yanzu dai jiragen ruwan na Rasha masu tafiya a karkashin ruwa sun bar yankin, kuma babu wata alamar an barnata kayayyakin more rayuwa da suke karkashin ruwa.
Da yake bayyana matakin a wani taro da manema labarai, Haeley yace an dauki matakan ne domin nunawa shugaba Vladimiri Putin cewa, an gane shirinsa.
Ahalinda ake ciki kuma, jiya Alhamis wani dan kasar Britaniya, mai suna Jermaine Grant, mai shekaru 43 da haifuwa ya bayyana a gaban kotu a birnin London, ana zarginsa da ta’addanci, cewa shi tsohon kwamanda ne a kungiyar al-shabab a Somalia.


