An Kafa Majalisar Kotun Sulhu Ta Kano
Hukumar kare hakkin dan Adam ta Najeriya tace kawancen aiki data kulla da Kotun Sulhu ta jihar Kano (Kano Multi-Door Court) yana haifar da sakamako mai kyau, ta fuskar warware matsalolin danne hakkoki a tsakanin al’uma. A taron kaddamar da sabbin mambobin majalisar kula da ayyukan Kotun, shugaban Ofishin shiyyar Kano na hukumar Abdullahi Shehu…

