Tsohon Antoni Janar kuma ministan shari’ar Najeriya Abubakar Malami, ya shafe kwana na biyu a tsare a hannun Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) bayan kasa cika sharuddan belinsa.
Majiyoyi sun ce ana bincikensa kan zarge-zargen laifuka 18, ciki har da hada hadar kuɗi da saba ka’idar aikin ofis, da kuma zargin taimakawa ayyukan ta’addanci ta hanyar kuɗi.
Hakanan, ana tuhumar sa kan yadda aka yi asarar dala miliyan $346.2 na kudin Abacha da aka dawo dasu daga Switzerland da Jersey, da kuma rabon kudaden shirin Anchor Borrowers na Naira biliyan 4.
EFCC na kuma binciken zargin cewa Malami ya zuba Naira biliyan 10 a makarantu, otal-otal da injinan shinkafa a Kebbi, tare da duba akalla asusun banki 46 da ake zargin suna da alaka da shi.
Malami, wanda ya koma jam’iyyar ADC a 2025, ya bayyana aniyarsa ta takarar gwamnan jihar Kebbi a 2027.
Jaridar The Cable ta kuma tunatar da wasu manyan mu’amaloli biyar da ake zargin sun faru a lokacin da Malami ke ofis, ciki har da biyan dala miliyan $496 ga GSHL a batun Ajaokuta, da sayar da kadarorin da aka kwace, da kuma rikicin biyan dala miliyan $419 ga masu neman diyya na Paris Club.


