Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Fargaba Ta Karu Duk Da Tsagaita Wuta Tsakanin Iran Da Amurka
Published: April 8, 2026 at 7:16 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Fargaba ta ƙaru duk da tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran

Natsuwa da aka samu bayan tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran ya sauya zuwa fargaba a ranar Laraba, yayin da rikici ke ci gaba da ƙamari a yankin, inda Israel ta kaddamar da hare-hare mafi girma zuwa yanzu kan Lebanon, sannan Iran ta kai hari kan cibiyoyin mai na ƙasashen yankin Tekun Fasha.

Kasuwannin kuɗi na duniya sun tashi bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da yarjejeniyar a ƙarshen jiya Talata, sa’o’i biyu kafin wa’adin da ya bai wa Iran domin buɗe mashigar Hormuz da aka killace, ko kuma ta fuskanci abin da ya kira lalata “dukkan wayewarta”.

Sai dai duk da cewa Israel da Amurka sun dakatar da hare-hare kan Iran, Isra’ila ta ƙara tsananta yaƙinta na daban a Lebanon, inda ta kaddamar da hare-hare mafi muni zuwa yanzu, lamarin da ya haifar da rudani a Beirut yayin da gine-gine ke rushewa.

Ministan lafiya na Lebanon ya ce mutane da dama sun mutu, yayin da daruruwa suka jikkata. Mazauna yankin sun ce wasu hare-haren Isra’ila sun zo ba tare da gargadin da aka saba bayarwa ga fararen hula domin su tsere ba.

Kamfanin dillancin labarai na Iran, Tasnim News Agency, ya rawaito wata majiya da ba a ambaci sunanta ba na gargadin cewa Iran za ta janye daga tsagaita wuta idan har hare-haren kan Lebanon suka ci gaba.

Afrika, Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Kasashen Amurka,Israela Da Iran Sun Amince Da Dakatar Da Yaki

Karin Labarai Masu Alaka

Amurka Da Iran Sun Cimma Yarjejeniya Tsagaita Wuta Na Makonni Afrika
Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki Labarai
China Ta Dawo Da Harajin Magungunan Hana Haihuwa Labarai
‘Yan Kasashen Afirka Da Dama Suna Fafatawa Da Rasha A Yaki Da Ukraine Afrika
Shugaban Amurka Ya Sauke Antoni Janar Amurka
‘Yan Bindiga Sun Kashe Dan Gaddafi A Gidansa Dake Kasar Libya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Fargaba Ta Karu Duk Da Tsagaita Wuta Tsakanin Iran Da Amurka
  • Kasashen Amurka,Israela Da Iran Sun Amince Da Dakatar Da Yaki
  • Gwamna Inuwa Yahaya ya Rusa Majalisar Zantaswa ta Jihar Gombe
  • Rundunar Sojin KTK Ta Harba Makami Teku
  • An Garkame Wani Babban Soja A Kasar Australiya

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaban Amurka Donald Trump Ya Nanata Aniyar Mallakar Greeland Daga Kasar Denmark Amurka
  • Amurka Da Tarayyar Turai Sun Fidda Sanarwa Afrika
  • Ma’aikatan Tattara Kudin Haraji Sunyi Rikici Da Masu Babura A Bauchi Najeriya
  • Rwanda Tana Keta Yarjejeniyar Zaman Lafiya – Tshisekedi Labarai
  • Gwamnatin Bauchi: Ba Zamu Bude Makarantu Ba Sai 2026 Labarai
  • Gwamna Kefas Na Jihar Taraba Ya Karbi Shaidar Jam’iyar APC Siyasa
  • Kudin Man Fetur Ya Karu Da Kashi 10 Cikin 100 Afrika
  • ‘Yan Sandan Najeriya Sunyi Nasarar Hallaka ‘Yan Ta’adda A Katsina Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.