Gwamnatin Jihar Adamawa aa amince da naira Biliyan 583.3 a matsayin kasafin kuɗi na shekarar 2026.
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, da majalisar shi ta amince da tsarin kasafin kuɗi na naira biliyan 583,331,380,496, a 2026, wanda aka yi wa take da “Kasafin Ci Gaba Mai Ɗorewa da Sabuntawa”.
Kasafin ya tanadi naira biliyan 209.64 (kashi 35.93) a matsayin kuɗaɗen gudanarwa, yayin da za a kashe naira biliyan 373.69, (kashi 64.07) kan ayyukan raya ƙasa, abin da ke nuni da fifikon da gwamnati ta bai wa manyan ayyukan ci gaba.
A zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar da Mataimakiyar Gwamna, Farfesa Kaletapwa G. Farauta, ta jagoranta, majalissar ta kuma jajanta wa al’ummar Karamar Hukumar Lamurɗe, tare da kira ga jama’a da su rungumi zaman lafiya da haɗin kai. Haka kuma, an shawarci al’umma da su kasance masu lura da tsaro ta hanyar gano baƙi a cikin unguwanninsu.
Daga cikin muhimman ayyukan da aka amince da su akwai gina cikakkun filayen wasanni a Kwalejin Fasaha, Ƙirƙira da Nazarin Kasuwanci da ke Gulak kan kuɗin Naira Biliyan 1.78; da kuma gina Ginin Babbar Kotun Jiha a Gulak, Karamar Hukumar Madagali, kan Naira Miliyan 373.77, da wa’adin kammalawa na watanni shida.
Majalisar ta kuma amince da gina Sakatariyar Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Adamawa a kan Naira Biliyan 2.50, wadda za a kammala cikin watanni 12. Sauran ayyukan sun haɗa da gina hanyar kilomita 2.2 daga Sangere Bode zuwa wasu matsugunnai a Yola South kan Naira Miliyan 290.31, da kuma hanya mai nisan kilomita 8.5 daga titin Numan zuwa Jalingo zuwa Kodomti da Shaforon a kan Naira Biliyan 1.89.
Haka zalika, gwamnatin ta amince da aikin gina katangar bulo ta Jami’ar Jihar Adamawa, Mubi, a kan kuɗin Naira Biliyan 3.53.


