Kakakin majalisar dokokin jihar Rivers a Najeriya, Martins Amaewhule, ya zargi gwamna Siminalayi Fubara da tauye tafiyar dimokuraɗiyya a jihar.
Amaewhule ya yi wannan zargi ne a ranar Alhamis, jim kaɗan bayan majalisar ta fara shirin tsige gwamnan da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, bisa zargin aikata manyan laifuka.
A cewar kakakin, ɓangaren zartarwa na gwamnati ya kasa bin tanade-tanaden kundin tsarin mulki sau da dama, musamman dangane da gabatar da kasafin kuɗi da amincewa da kashe kuɗaɗe.
“Babu wani abu da ke hana gwamnati gabatar da kasafin kuɗi da gangan ya zaɓi ƙin yin hakan,” in ji Amaewhule.
Ya ce gwamnan na faɗa wa magoya bayansa cewa wannan majalisa ba ta da wani ƙarfi, yana kiranta da “kare mara haƙora”, yana kuma cewa Majalisar Dokoki ta 10 ba za ta iya yin komai ko tilasta bin kundin tsarin mulki ba.
Amaewhule ya bayyana lamarin a matsayin mai haɗari ga dimokuraɗiyya a jihar Rivers.
“Wannan abin takaici ne ga dimokuraɗiyyarmu, Sir Siminalayi Fubara da Farfesa Ngozi Odu barazana ne ga dimokuraɗiyyarmu kuma idan aka bar su suka ci gaba da wannan hali, ina fargabar abin da zai faru da tafiyar dimokuraɗiyya a jihar Rivers,” in ji shi.
Ya kuma zargi gwamnan da mataimakiyarsa da kashe kuɗaɗen jama’a ba tare da amincewar Majalisa ba.
“Suna yawo daga wuri zuwa wuri suna kashe kuɗaɗen masu biyan haraji ba tare da amincewar majalisa ba,” in ji Amaewhule.


