Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Guinea An Zabi Madugun Sojojin Da Suka yi Juyin Mulki Mamady A Shugaban Ƙasar,
Published: January 1, 2026 at 10:31 AM | By: Bala Hassan

 Ƙasar Guinea kuma an zabi Mamady Doumbuya, madugun sojojin da suka yi juyin mulki a zaman shugaban kasa, kamar yadda kwarya-kwaryar sakamakon zabe da aka bayyana jiya talata, mataki da ya kammala shirin maido da kasar kan turbar demokuradiyya, ga kasar dake Afirka ta yamma da Allah Ya yiwa albarkar karfe. 

Tsohon kwamandan dakaru na musamman, wanda ake kiyasin dan shekaru 40 ne da haifuwa, Dumbouya ya yiwa shugaba Alpha Conde wanda yake shugabancin kasar tun 2010 juyin mulki shekara ta 2021. Juyin mulkin na kwango yana daga cikin jerin sauye sauye gwamnati da bakin bindiga har tara a kasashe da suke yammaci da kuma wadanda suke yankin tsakiyar Afirka daga shekara ta 2020.

Kwarya-kwaryar sakamakon zaben da aka bayar a  talata, ya nuna shugaba Doumbuya ya sami kashi 86.7 cikin dari na kuriu da aka kada, a zaben da aka yi ranar 28 ga watan Disemban 2025, rinjaye mai karfi da zata hana shi zuwa zagaye na biyu a zaben,

Tuni dai ake sa ran shugaba Doumbuya ya sami nasara a zaben, domin tsohon shugaban kasa Alpha Conde, da dadadden shugaban ‘yan hamayya Cellou Dalein Diallo suke gudun hijira, wadda ya baiwa shugaba Doumbuya damar fuskantar tsirarun ‘yan hamayya da suka kasa hada kai su takwas.

Kotun kolin kasar tana da kwanaki takwas ta tabbatar da sakamakon zaben, idan har akwai wadanda suke jayayya kan wannnan sakamako.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: ‘Yansandan Uganda Sun Tsare ‘Yar Fafutukar Kare Hakkin Bil’adama Sarah Bireete
Next Post: Tinubu Yace Zayyi Hadaka Da Kasashen Duniya Domin Kawo Karshen Rashin Tsaro.

Karin Labarai Masu Alaka

CAF Ta Yanke Hukunci Kan Ƙasashen Senegal Da Moroko AFCON 2025 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Shahararren Dan Dambe Anthony Joshua Yayi Hatsarin Mota A Jihar Ogun Labarai
Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Gwamnatin Gombe Ta Dauki Sabbin Matakan Tsaro Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Wata Tankar Mai Ta Kife A Apapa Legas Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Jihohin Arewaci Sun Kafa Asusun Yaki Da Ta’addanci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Jami’ai Daga Amurka Sunce Yakin Amurka Da Iran Zaizo Karshe
  • An Gudanar da Taron Kwana Biyu kan Tsarin Sa Ido da Tantance Ayyukan AGILE a Jihar Gombe 
  • Rwanda Zata Janye Dakaru Daga Mozambique
  • Ruwan Sama Yayi Ajalin Mutane 70 A Nairobi
  • Shugaban Amurka Yayi Watsi Da Tattaunawar Kawo Karshen Yaki Da Iran

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Kasar Ghana Ta Bayyana Fataucin Bayi A Matsayin Babban Laifi Afrika
  • Gwamnatin Tarayya Na Kokarin Hana Demokraɗiyya A Najeriya Siyasa
  • Mace Ta Farko Da Zata Shugabanci Jami’ar Northwest Dake Kano Najeriya
  • Shugaban Ƙasar Koriya Ta Arewa Ya Halarci Gwajin Makami Mai Linzamin Kasar Labarai
  • Kungiyar EU Zata Taimakawa Somalia Da Kudade Labarai
  • Najeriya Ta Gabatar Da Tayin Karbar Bakoncin Wasannin Afirka Na 2031 Wasanni
  • Ko Arsenal Zata Iya Lashe Gasar Firimiya lig Na Bana Wasanni
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.