Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • An Bawa Fasto Yohanna Buru Sarautar “Jagoran Zaman Lafiyar Arewacin Najeriya” Afrika
  • Inuwa Yahaya Ya Yi Alkawarin Barin Gombe Ba Tare Da Bashin Fansho Ba Afrika
  • NBA Gombe Ta Nemi IGP Ya Binciki Zargin Karɓar Kuɗi A FCID Annex Gombe Afrika
  • Ɗalibai 670 Sun Amfana Da Tallafin Jakakkuna Da Littattafai Daga Hukumar NEDC A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Gombe Ta Ƙarfafa Matakan Kare Dabbobi Daga Cututtuka Afrika

Gurbin Yaya Tongo: INEC Ta Tsayar Da 19 Ga Satumba Don Zaɓen Cike Gurbi
Published: August 19, 2026 at 1:03 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta a Najeriya wato (INEC) ta tsayar da Asabar, 19 ga Satumba, 2026 a matsayin ranar da za a gudanar da zaɓen cike gurbin kujerar wakiltar Gombe/Kwami/Funakaye a Majalisar Wakilan Tarayya.

Za a gudanar da zaɓen ne domin cike gurbin da ya samu sakamakon rasuwar ɗan majalisar da ke wakiltar mazabar, Honarabul Yaya Bauchi Tongo, wanda ya rasu yana da shekaru 62 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

INEC ta bayyana cewa za a gudanar da zaɓen ne bisa tanadin Sashe na 76(2) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, kamar yadda aka yi wa gyara, da kuma sauran tanade-tanaden dokar zaɓe.

A cikin jadawalin da hukumar ta fitar, za a wallafa Sanarwar Zaɓe a ranar Alhamis, 20 ga Agusta, 2026.

Hukumar ta kuma tsara cewa jam’iyyun siyasar da ke da niyyar tsayar da ’yan takara su gudanar da zaɓen fidda gwani tsakanin 21 zuwa 25 ga Agusta, 2026.

Bayan kammala zaɓen fidda gwani da sauran matakan tantance ‘yan takara, INEC za ta wallafa jerin sunayen ’yan takarar da aka amince da su a ranar 8 ga Satumba, 2026.

A cewar jadawalin, yakin neman zaɓe na hukuma zai fara ne a 9 ga Satumba, sannan ya ƙare a 17 ga Satumba, 2026, kwanaki biyu kafin ranar zaɓen.

Mazabar Gombe/Kwami/Funakaye ta ƙunshi Kananan Hukumomi uku, wato Gombe, Kwami da Funakaye. INEC ta ce za a gudanar da zaɓen a faɗin rumfunan zaɓe 903 da yankunan rajista 31 na mazabar.

Hukumar ta yi kira ga dukkan jam’iyyun siyasa da ’yan takararsu da su bi jadawalin da aka tsara tare da gudanar da dukkan harkokinsu cikin bin dokokin zaɓe.

INEC ta kuma tabbatar wa masu ruwa da tsaki a mazabar cewa tana da cikakken shiri na gudanar da zaɓe cikin ’yanci, adalci da gaskiya, tare da samar da dama iri ɗaya ga dukkan jam’iyyun siyasa da ’yan takara.

Hukumar ta kuma yi kira ga masu kada kuri’a da su fito su gudanar da haƙƙinsu na ɗan ƙasa cikin lumana da sanin ya kamata.

Zaɓen na ranar 19 ga Satumba, 2026 na daga cikin zaɓukan cike guraben kujerun majalisun dokokin da INEC ta tsara gudanarwa a wasu jihohin Najeriya.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Shirye-Shirye, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Manchester United Na Dab Da Kammala Daukar Carlos Baleba Daga Brighton
Next Post: Kuɗaɗen Da EFCC Ta Kwato Za Su Tallafa Wa Shirin Lamunin Karatu

Karin Labarai Masu Alaka

Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo Ya Ziyarci IBB Siyasa
Sojojin Kasar Uganda Sun Bazama Neman Bobi Wine Sakamakon Rikicin Bayan Zabe Siyasa
Aminu Tambuwal Ya Fice Daga PDP Ya Koma ADC Afrika
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Gombe Ya Ziyarci Pindiga Labarai
Suvr Jahun: Ya Kamata Obasanjo Ya Bar Al’umar Ƙasa Su Fito Da Wadda Suke So 2027 Najeriya
Hamma Saleh Ya Yi Fatali da Bai Wa Pantami Takarar Gwamna a PDP Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • An Bawa Fasto Yohanna Buru Sarautar “Jagoran Zaman Lafiyar Arewacin Najeriya”
  • INEC TA Fitar Da Jerin ’Yan Takarar Gwamnan Gombe, Ba A Ga Sunan Sheikh Pantami Ba
  • Inuwa Yahaya Ya Yi Alkawarin Barin Gombe Ba Tare Da Bashin Fansho Ba
  • NBA Gombe Ta Nemi IGP Ya Binciki Zargin Karɓar Kuɗi A FCID Annex Gombe
  • Ɗalibai 670 Sun Amfana Da Tallafin Jakakkuna Da Littattafai Daga Hukumar NEDC A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • INEC TA Fitar Da Jerin ’Yan Takarar Gwamnan Gombe, Ba A Ga Sunan Sheikh Pantami Ba Labarai
  • Kasar Ukraine Tayi Watsi Da Shiga Kungiyar NATO Labarai
  • Rundunar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Shirya Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Jihar Filato Afrika
  • Najeriya Da Poland Za Su Hada Kai Kan Tsaro da Bunƙasa Tattalin Arziki Afrika
  • Hawan Durba A Fadar Sarkin Zazzau Afrika
  • Samar Da Tsaro A Jihar Kano Ba Sai An Sa Siyasa Ba! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kamfanin Hakar Ma’adanai Na Kasar Kanada Ya Cigaban Da Aikinsa Labarai
  • Masarautar Borgu a Jihar Neja na neman daukin Gwamnatin Najeriya akan matsalar rashin tsaro Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.