Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • NIHSA Ta Yi Gargadin Ambaliyar Ruwa A Jihohi 15 Afrika
  • Gidauniyar Misilli Ta Tallafa Wa Yara Da Dattawa A Gombe Afrika
  • Laccar Bagauda Kaltho Ta Jaddada Muhimmancin Yaƙi Da Yaɗa Labaran Karya Afrika
  • Cutar Mashako: Gwamnatin Gombe Ta Fara Rigakafin Gaggawa A Makarantu Kiwon Lafiya
  • NUJ Ta Kai Ziyarar Jaje GMC Bayan Gobara Ta Lalata Ginin Sashen Talabijin Afrika

Gwamna Inuwa Yahaya Ya Jaddada Haƙuri Da Fahimtar Juna A Siyasa
Published: August 30, 2026 at 2:19 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi kira ga al’ummar jihar da su kasance masu haƙuri, haɗin kai da zaman lafiya a harkokin shugabanci da siyasa.

Gwamnan ya kuma bukaci jama’a da su guji ƙiyayya, kalaman rarrabuwar kai da duk wani abu da ka iya haifar da tashin hankali a tsakanin al’umma.

Inuwa Yahaya ya yi wannan kiran ne a wajen rufe gasar haddar Alƙur’ani da karatunsa karo na 29, wadda Ƙungiyar Izala Assasawar Sheikh Ismaila Idris Jos ta shirya a garin Bambam, ƙaramar hukumar ci gaban Balanga ta Kudu a Jihar Gombe.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ne ya wakilci gwamnan a wajen taron.

Gwamna Yahaya ya yaba wa ƙungiyar bisa kokarin da take yi wajen tarbiyyantar da matasa ta fuskar addini da kuma bunƙasa karatun Alƙur’ani.

Ya tabbatar wa masu shirya gasar cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen da ke inganta ɗabi’u da tarbiyya, tare da samar da al’umma masu tsoron Allah da sanin nauyin da ke kansu.

Gwamnan ya kuma jaddada muhimmancin goyon bayan al’umma ga gwamnatinsa, yana mai cewa nasarorin da Jihar Gombe ta samu a shekarun baya sun samu ne sakamakon haɗin kai da goyon bayan jama’a.

Ya yi kira ga al’umma da su kasance masu natsuwa, tare da guje wa kalamai ko ayyukan da za su iya haddasa tashin hankali, kawo rabuwar kai ko barazana ga zaman lafiyar jihar.

Ya ce haɗin kai da fahimtar juna tsakanin al’umma na da matuƙar muhimmanci wajen ci gaba da ɗorewar ci gaban Jihar Gombe.

Gwamnan ya ƙara da cewa nasarorin da jihar ta samu sun jawo hankalin wasu jihohi, waɗanda ke ƙara nuna sha’awa ga tsarin ayyukan raya ƙasa da Gombe ta fara aiwatarwa.

Tun da farko, Shugaban Majalisar Ulama ta Ƙungiyar Izala, Sheikh Hamza Abdulhamid, ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da yi wa shugabanninsu addu’a tare da nuna haƙuri da juriya.

Malamin ya ce ƙungiyar Izala ta daɗe tana taka rawa wajen ilmantar da Musulmi, inda ta kafa makarantu a matakai daban-daban, tare da shirin kafa jami’a domin ci gaba da bunƙasa ilimin addini da na zamani.

Sheikh Hamza ya kuma yi gargadi kan kalaman rarrabuwar kai da rikice-rikicen da ba su da amfani, yana mai cewa bambancin ra’ayin siyasa bai kamata ya zama sanadin ƙiyayya ko gaba tsakanin ‘yan kasa ba.

Ya bukaci jama’a da su rungumi tattaunawa, haƙuri da zaman lafiya, yana mai cewa siyasa ya kamata ta zama hanyar warware bambance-bambance, ba kuma hanyar haifar da rikici ba.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Gwamnan Bauchi Ya Shiga Neman Mafita Kan Lalacewar Matatar Ruwan Alkaleri
Next Post: Damara Ya Tallafa Wa Gasar Karatun Al-Qur’ani Da Naira Miliyan Biyar A Bambam

Karin Labarai Masu Alaka

Jirgin Sama Ya Fadi A Kano Labarai
Tinubu Ya Nada Shugabannin Hukumar NERC Najeriya
‘Yan Kungiyar Boko Haram Sun Yi Awon Gaba Da Mata 13 A Borno Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Jirgin Ruwa Ya Kife A Yammacin Kasar Gambiya Labarai
Dan Ra’ayin Mazan Jiya Leo Brent Zai Kyautata Alakar Afirka Ta Kudu Da Amurka Afrika
Mayakan Boko Haram Da ISWAP Sun Kai Hari Cikin Dare Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • NIHSA Ta Yi Gargadin Ambaliyar Ruwa A Jihohi 15
  • Gidauniyar Misilli Ta Tallafa Wa Yara Da Dattawa A Gombe
  • Laccar Bagauda Kaltho Ta Jaddada Muhimmancin Yaƙi Da Yaɗa Labaran Karya
  • Cutar Mashako: Gwamnatin Gombe Ta Fara Rigakafin Gaggawa A Makarantu
  • NUJ Ta Kai Ziyarar Jaje GMC Bayan Gobara Ta Lalata Ginin Sashen Talabijin

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Trump Yayi Barazanar Tarwatsa Cibiyar Makamashin Iran Amurka
  • Shugaban Kasar Ivory Coast Yayi Sauye-Sauye A Majalisar Ministocin Kasar Siyasa
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • Ana Cigaba Da Bincike Game Da Mutuwar Matar Da Likita Ya Manta Almakashi A Cikinta A Kano Najeriya
  • Na Duke Tsohon Ciniki Shirye-Shirye
  • Hukumomi A Kasar Syri Lanka Suna Kokarin Fidda Jirgin Yakin Iran Daga Kasar Afrika
  • Shugaba Trump Yace Amurka Da Iran Suna Cigaba Da Tattaunawa Amurka
  • Shugaba Tinubu Zai Shafe Makonni Uku A Hutun Shekara-Shekara Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.