Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Gwamnan Gombe Ya Taya Sarkin Musulmi Murnar Cika Shekaru 70, Ya Yi Masa Addu’ar Ƙarin Lafiya Da Tsawon Rai
Published: August 24, 2026 at 1:45 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Gombe kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya (NNGF), Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, ya taya Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Mai Alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar III, CFR, murnar cika shekaru 70 da haihuwa.

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana Sarkin Musulmin a matsayin babban jigo wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da haɗin kan al’umma a Najeriya, yana mai cewa kusan shekaru 20 na jagorancinsa sun yi matuƙar tasiri ga al’ummar Musulmi da kuma ƙasar baki ɗaya.

A cikin saƙon taya murna da ya aika a madadin gwamnonin jihohin Arewa 19, Gwamnan ya yaba da irin jagorancin da Sarkin Musulmi ke nunawa a matsayinsa na jagoran ruhaniya na Musulman Najeriya.

Ya ce Sultan Sa’ad Abubakar ya kasance mai ƙoƙari wajen inganta zaman lafiya, fahimtar juna tsakanin mabiya addinai, haƙurin addini da kuma haɗin kan al’umma a sassa daban-daban na ƙasar.

Gwamnan ya ƙara da cewa a tsawon shekaru, Sarkin Musulmi ya yi amfani da matsayinsa da tasirinsa wajen ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai tsakanin Musulmi, tare da yin aiki da sauran ƙungiyoyin addini, kabilu da sassa daban-daban na al’umma domin samar da fahimtar juna da haɗin kan ƙasa.

A cewar Gwamna Inuwa Yahaya, jajircewar Sarkin Musulmi wajen tabbatar da zaman lafiya da jituwa ta sanya shi zama ɗaya daga cikin manyan muryoyin da ake saurara a harkokin ƙasa, musamman wajen ƙoƙarin ƙarfafa shugabanci nagari, zaman lafiya da ci gaba.

Gwamnan ya ce, “A matsayinsa na mai kula da kyawawan al’adunmu da tarihimmu, Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya kasance mai jajircewa wajen inganta haɗin kai, zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai. Ƙoƙarinsa ya ƙarfafa haɗin gwiwa da zaman lafiya, tare da kare ginshiƙan zamantakewar al’ummarmu.”

Shugaban NNGF ya kuma yaba da shawarwari masu amfani da Sarkin Musulmi ke bayarwa, da kuma irin goyon bayan da yake bai wa ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya, tsaro da ci gaban Arewacin Najeriya.

Ya ce matsayinsa da shawarwarinsa kan muhimman batutuwan ƙasa sun taimaka wajen ƙarfafa ƙudurin shugabanni da sauran masu ruwa da tsaki na gina Arewa mai haɗin kai, zaman lafiya da wadata.

Gwamna Inuwa Yahaya ya buƙaci Shugaban NSCIA ya ci gaba da amfani da hikimarsa, mutuncinsa da tasirinsa wajen inganta zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba, ba kawai a Masarautar Sokoto da Arewacin Najeriya ba, har ma da faɗin ƙasar.

Gwamnan, wanda ke riƙe da sarautar gargajiya ta Dan Amanan Daular Usmaniyya, ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya ƙara wa Sultan Sa’ad Abubakar lafiya, hikima da ƙarfi, tare da ba shi tsawon rai domin ya ci gaba da hidimtawa al’ummar Musulmi, Najeriya da ɗaukacin bil’adama.

Saƙon taya murnar ya fito ne daga Ismaila Uba Misilli, Darakta-Janar mai kula da harkokin yaɗa labarai na Gidan Gwamnati. jihar Gombe.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
Next Post: Dan Wasan Baya Na Chelsea, Disasi, Zai Yi Gwajin Lafiyarsa A Crystal Palace

Karin Labarai Masu Alaka

Hukumar EFCC Ta Kwace Gidan Tsohon Antoni Janar Abubakar Malami Najeriya
Wata Tankar Mai Ta Kife A Apapa Legas Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Hukumar Kare Hakkin ‘Yan Jarida Tace Isra’ila Ce Ta Kashe ‘Yan Jarida Kashi Biyu Bisa Uku Labarai
Trump Da Bin Salman Da Wasu Kasashe Za Su Sa Hannu A Rikicin Sudan Labarai
Wani Harin ‘Yan Bindiga Ya Kashe Mutane 35 A Jihar Borno Labarai
Rundunar ‘Yan Sanda Ta Bukaci Al’umma Su Kiyaye Doka Yayin Bikin Takutaha Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Rundunar Sojin KTK Ta Harba Makami Teku Afrika
  • NLC Ta Yabawa Gwamnan Gombe Inuwa Yahaya Najeriya
  • Iran Zata Shigar Da Lebanon Cikin Cimma Yarjejeniya Afrika
  • Jami’an Diflomasiyyar Iran Dana Amurka Sun Tattauna A Kasar Oman Afrika
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Isra’ila Takai Sabon Hari Tehran Ranar Lahadi Labarai
  • Ankara Kai Wani Harin Bom Birnin Maiduguri Afrika
  • Shugabannin Miyetti Allah Sun Nemi Sa Hannun Gwamnoni Wajen Sako Bello Bodejo Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.