Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Gwamnan Jihar Gombe Ya Ƙarfafa Wa Sabbin Masu Ashaka Cement Gwiwar Samar Da Ayyukan Yi
Published: August 17, 2026 at 5:40 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, ya buƙaci shugabannin HBM Nigeria PLC, sabbin masu mallakar Kamfanin Ashaka Cement, da su daidaita shirin faɗaɗa samar da siminti da ƙara himma wajen kula da jin daɗin al’ummomin da ke karɓar bakuncin kamfanin da kuma kare muhalli.

Gwamna Inuwa Yahaya ya yi wannan kira ne a lokacin da ya karɓi tawagar kamfanin ƙarƙashin jagorancin Babban Darakta kuma Shugaban Kamfanin HBM Nigeria PLC, Mista Lolu Alade-Akinyemi, wanda ya kai masa ziyarar ban girma a Gidan Gwamnatin Jihar Gombe. Tawagar ta haɗa da Manajan Daraktan Ashaka Cement, Ibrahim Aminu.

Gwamnan ya ce shirin ƙara ƙarfin samar da siminti na Ashaka Cement wata dama ce da za ta bai wa kamfanin damar ƙara bayar da gudunmawa ga ci gaban tattalin arzikin Jihar Gombe, musamman ta hanyar samar da ayyukan yi, bunƙasa harkokin cikin gida, ci gaban al’umma da ƙarfafa shirye-shiryen tallafin al’umma na kamfani.

Ya tabbatar wa kamfanin cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da yin aiki kafada da kafada da HBM Nigeria PLC domin samar da yanayin da zai ba da damar samun ci gaban masana’antu mai ɗorewa.

Gwamnan ya bayyana cewa Ashaka Cement na da babban suna da karɓuwa a Arewacin Najeriya, yana mai buƙatar kamfanin ya yi amfani da wannan matsayi wajen ci gaba da kasancewa cikin manyan masu samar da siminti da sauran kayayyakin gini a ƙasar.

Ya jaddada cewa duk da cewa samun riba muhimmin buri ne ga kasuwanci, kamfanoni na da nauyin kula da al’ummomin da suke gudanar da ayyukansu a cikinsu da kuma kare muhalli.

Gwamnan ya kuma buƙaci HBM Nigeria PLC da ta duba yiwuwar inganta hanyoyin da suka haɗa da Ashaka Cement, yana mai cewa wasu daga cikin hanyoyin da gwamnatin jihar ta gina sun lalace sakamakon yawan manyan motoci da ayyukan ɗaukar kaya da ke da alaƙa da kamfanin.

Haka kuma, Gwamna Inuwa Yahaya ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa bayar da kwangilar gina babbar hanyar Gombe zuwa Biu, wadda ya bayyana a matsayin muhimmin aikin raya ƙasa da zai amfani al’ummar Gombe da kuma masana’antu da ’yan kasuwa a yankin.

Ya buƙaci Ashaka Cement ta shirya domin samar da simintin da za a buƙata wajen gina babbar hanyar, musamman ganin cewa ana sa ran za a yi amfani da shimfiɗar siminti wajen aikin.

A nasa jawabin, Babban Darakta kuma Shugaban HBM Nigeria PLC, Lolu Alade-Akinyemi, ya bayyana cewa sauya sunan kamfanin daga Lafarge Africa PLC zuwa HBM Nigeria PLC ya biyo bayan shigar Lafarge cikin Huaxin Building Materials Group, wani shahararren kamfanin duniya da ke kera siminti da kayayyakin gini.

Ya tabbatar wa Gwamna Inuwa Yahaya cewa, duk da sauyin mallaka, jajircewar kamfanin ga gwamnatin Jihar Gombe da al’ummarta ba za ta sauya ba.

Akinyemi ya ce sabon shugabancin kamfanin zai ba da fifiko ga amfani da kayayyakin cikin gida, haɗin gwiwar dabaru, ci gaban al’umma da shirye-shiryen tallafin kamfani, tare da ƙara gudunmawarsa ga tattalin arzikin jihar.

Ya bayyana cewa ana shirin ƙara ƙarfin samar da siminti na Ashaka Cement zuwa tan miliyan biyu a kowace shekara, matakin da ya ce zai samar da ƙarin guraben ayyukan yi tare da bunƙasa harkokin tattalin arziki ga masu sufuri, masu samar da kayayyaki da sauran ‘yan kasuwa da ke cikin jerin masu cin gajiyar ayyukan kamfanin.

Babban Daraktan ya kuma yaba wa Gwamna Inuwa Yahaya bisa kyakkyawan shugabanci da kuma samar da yanayin da ya dace domin bunƙasa ababen more rayuwa, tattalin arziki da masana’antu a Jihar Gombe.

Ya ƙara tabbatar da shirye-shiryen kamfanin na ƙarfafa haɗin gwiwa da gwamnatin jihar da kuma ƙara bayar da gudunmawa wajen ci gaban Gombe da walwalar al’ummarta.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sana'o'i, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Kamaru Ta Lallasa Malawi 3-0, Ta Lashe Kofin WAFCON Na Farko A Tarihi
Next Post: NFF, Ta Umarci Tawagar Masu Horas Da Super Falcons Su Sauka Daga Bakin Aiki Nan Take

Karin Labarai Masu Alaka

Kungiyar Kiristoci Ta Karyata Kubutar Da Mambobin Su A Kaduna Afrika
Maulidi: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar Hutu Afrika
An Tsinci Gawar Yarinya A Gombe Najeriya
Harin Jirgi Marar Matuki Ya Kashe Kakakin ‘Yan Tawayen M23 Afrika
Tinubu Ya Kawo Ƙarshen Aikin Kwamitin Sayar Da Kaddarorin Gwamnati Afrika
Gwamna Abba Gida-Gida Na Dari-Darin Shiga APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Majalisar Wakilai Tayi Allah Wadai Da Hare-Haren ‘Yan Bindiga A Gombe Labarai
  • Hukumomin Tsaron Kenya Sunce ‘Yan Kasar Suna Fafata Yaki Da Dakarun Rasha A Ukraine Afrika
  • Diphtheria: Mutane 23 Sun Mutu A Jihar Filato Afrika
  • Wasan Dambe Ya Dau Sabon Salo A Jihar Inugu Wasanni
  • Kungiyar ISIS Ta Dauki Alhakin Harin Kasar Nijar Afrika
  • Shugaba Tinubu Ya Gana Da Wasu Gwamnoni Shida Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Sanatan Nasarawa Ta Arewa Ya Rasu A Kasar India Najeriya
  • Wasu Mutane 15 Sun Rasa Rayukan Su A Gabashin Kwango Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.