Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maikaba Ya Yi Murabus A Matsayinsa Kocin Wikki Tourist FC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NEDC : Zata Samar Da Cikekken Kulawa Wa ‘Yan Jaridar Da Sukayi Hatsari A Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Trump Zata Kafa Kasuwar Ma’adanai Amurka
  • An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Babban Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Gwamnan Jihar Kano Ya Fice Daga Jam’iyar NNPP
Published: January 23, 2026 at 4:16 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), yana mai danganta matakin da tsanantar rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyar da kuma buƙatar kare muradun al’ummar jihar Kano gaba ɗaya.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Juma’a.

A cikin wasiƙar da ya aike wa Shugaban mazabar Diso-Chiranchi na jam’iyyar NNPP a Ƙaramar Hukumar Gwale, gwamnan ya sanar da janyewarsa daga jam’iyyar, wanda zai fara aiki daga ranar Juma’a, 23 ga Janairu, 2026.

“Ina rubuta wannan wasiƙa cikin matuƙar godiya domin sanar da shugabannin jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) cewa na yanke shawarar ajiye kasancewata ɗan jam’iyyar, daga ranar Juma’a, 23 ga Janairu, 2026.”

Gwamna Yusuf ya bayyana godiyarsa ga jam’iyyar bisa damar da ta ba shi da kuma goyon bayan da ya samu tun farkon tafiyarsa ta siyasa a ƙarƙashin NNPP.

Ya kuma yi nuni da cewa jam’iyyar na fuskantar rikice-rikice na cikin gida da kuma ƙalubalen shari’a da suka daɗe suna dagula tsarinta a matakin ƙasa.

A cewarsa, rikice-rikicen sun haifar da rarrabuwar kawuna tare da raunana haɗin kan jam’iyyar.

Gwamnan ya ce ya ɗauki matakin ne bayan zurfin nazari, kuma bisa la’akari da muradun jama’a kawai.

Ya jaddada cewa ya ɗauki wannan mataki ne cikin kyakkyawar niyya ba tare da wata ƙiyayya ba.

“Na ɗauki wannan mataki cikin kyakkyawar niyya, ba tare da wata muguwar manufa ko ƙiyayya ba, tare da ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban jihar Kano.”

Gwamnan ya fice tare da mambobi 21 na Majalisar Dokokin jihar Kano, mambobi 8 na Majalisar Wakilai ta Tarayya, da kuma shugabannin ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano.

Sakataren jam’iyyar NNPP na Ward ɗin Diso-Chiranchi, Kabiru Zubairu, ya tabbatar da karɓar wasiƙar tare da yabawa gwamnan bisa ayyukan ci gaba da ya aiwatar a fannoni daban-daban.

Siyasa

Post navigation

Previous Post: Tsohon Lauyan Amurka Jack Smith Ya Fadi Maganganu Game Da Donald Trump
Next Post: Kasar Uganda Ta Tsare ‘Yan Jam’iyyun Adawa Dubu Biyu

Karin Labarai Masu Alaka

PDP Zata Karbi Mulki 2027 Inji Shugabannin Jam’iyar Siyasa
An Sako Dan Siyasar Kasar Venezuela Daga Gidan Yari Labarai
Kauran Gwandu Zai Inganta Wutan Lantarki A Kebbi Siyasa
Ana Gudanar Da Zanga-Zangar Adawa Da Gwamnati A Kasar Tunisiya Siyasa
Jam’iyar APC A Najeriya Ta Kaddamar Da Bada Shaidar Zama Dan Jam’iyyar Ta Na’ura Mai Kwakwalwa Siyasa
Samar Da Tsaro A Jihar Kano Ba Sai An Sa Siyasa Ba! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Muna Kokarin Kawo Karshen Cin Zarafin Jinsi A Gombe – Uwargidan Gwamna
  • Majalisar Dattawar Najeriya Ta Amince Da Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet
  • Yeriman Ingila Ya Gana Da Yeriman Saudiya Mai Jiran Gado
  • Dubban Mutane Sunyi Zanga-Zanga A Kasar Australia
  • Bangladesh Tasamu Rangwamen Harajin Da Amurka Ta Kakaba Mata

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Darajar Kudin Afirka Ta Kudu Ya Tashi Afrika
  • Marc Brys: “Eto’o Baiyi Adalci Ga Onana, Da Vincent, Ba” Wasanni
  • Kasar Iceland Ta Kauracewa Bikin Gasar Wakokin Shekara Mai Zuwa Labarai
  • ‘Yan Sanda Sun Kama Masu Garkuwar da Mutane a Jihar Gombe Tsaro
  • ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane A Kauyuka Dake Yammacin A Najeriya Najeriya
  • Sabunta Manhajar Ilimi A Duk Matakai Nasara Ce! Najeriya
  • Shahararren Dan Dambe Anthony Joshua Yayi Hatsarin Mota A Jihar Ogun Labarai
  • Dan Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Atiku Abubakar Ya Shiga Jam’iyyar APC Siyasa
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.