Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Gwamnatin Gombe Ta Kulla Yarjejeniyar Da New Zealand
Published: February 4, 2026 at 9:47 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin jihar Gombe ta ɗauki wani muhimmin mataki na zamanantar da harkokin kiwon dabbobi ta hanyar sanya hannu kan wata muhimmiyar yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da Cibiyar Zamanantar da Kiwo (LIC) a Ƙasar New Zealand.

Haɗin gwiwar na da nufin bunƙasa kiwo, da ƙarfafa jure sauyin yanayi da kuma buɗe sabbin damammakin tattalin arziƙi a duk sassa da sana’o’in da suka jiɓinci kiwon dabbobi.

Yarjejeniyar ta biyo bayan ziyarar aiki ce ta kwanaki biyu da wata babbar tawagar jihar Gombe ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ta kai a cibiyoyin haɓaka kiwo na zamani na LIC dake birnin Hamilton, na ƙasar ta New Zealand.

A ƙarƙashin yarjejeniyar, ɓangarorin biyu za su yi aiki tare kan haɓaka tsarin bayanai da fasahar zamani don kula da dabbobi, da haɓaka dabarun aiki masu ɗorewa, da kuma ƙarfafa cibiyoyi ta hanyar horaswa da musayar ilimi.

Yarjejeniyar ta kuma samar da tsarin ayyukan bincike na haɗin gwiwa, ciki har da haɗin gwiwa da Jami’ar jihar Gombe, da binciko damammaki a fannin fasahar kwayoyin halitta da fasahar ririta halittu, kamar samar da ingantattun irin shanun madara dana nama na ƙasar ta New Zealand, bisa ga amincewar hukumomi.

Don tabbatar da ingantaccen aiwatarwa da samar da sakamako mai ma’ana, za a kafa tawagar aiki da cikawa ta haɗaka don kula da ayyukan, da samar da tsare-tsaren aiki daki-daki da kuma sanya ido kan nasarorin da ake samu.

Tattaunawar ranar farko ta mayar da hankali ne kan kyakkyawan tsarin kula da dabbobi, da tsarin samar da kayayyaki mai ɗorewa, da kuma gyare-gyaren da za a yi a fannin na dogon lokaci.

A rana ta biyu, tawagar ta kai rangadin aiki a gonar zamani ta LIC, inda aka sanya hannu kan yarjejeniyar a hukumance.

Da yake jawabi a wurin bikin sanya hannun, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana ƙawancen a matsayin wani babban ci gaba a tsarin sauya fasalin noma da kiwo na Jihar Gombe.

Tawagar Gomben ta samu goyon bayan gwamnatin tarayya daga Ministan Bunƙasa Kiwo, Alhaji Mukhtar Maiha, wanda ya jaddada goyon bayan gwamnatin tarayya ga wannan shiri.

A cewarsa, haɗin gwiwar yana nuna kyakkyawar alkiblar manufofin gwamnatin Tinubu.

Ministan ya ce, “Wannar haɗin gwiwa ta yi daidai da Ƙudurin Sabunta Fata, wadda ke jaddada amfani da fasaha, ɗorewar tsare-tsare da kuma ganin tasirinsu kan tattalin arziki a zahirance.”

“Za mu ci gaba da tallafawa matakan da suka wuce furucin manufofi kawai don samar da fa’idoji na gaske ga manoma da tattalin arziƙin ƙasa.”

A madadin Cibiyar Haɓaka Kiwon Dabbobin, Manajan Bunƙasa Kiwo na Duniya Jason Schrier ya yi maraba da wannar haɗin gwiwa, yana mai bayyana ta a matsayin haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa abar koyi ga a fannin haɓaka kiwo.

“Muna alfahari da karbar baƙuncin tawagar Jihar Gombe da kuma yin aiki tare don samar da sabuwar makoma ga harkar kiwo a Jihar Gombe da Najeriya,” in ji shi.

“Ina farin cikin cewa wannar yarjejeniyar ta haɗa da ƙwarewar fasaha ta LIC da kuma kyakkyawan shugabanci na Jihar Gombe da kuma ƙudurin gyara da Mai Girma Gwamna ya tsara.”

Gwamna Inuwa Yahaya ya samu rakiyar manyan jami’ai, ciki har da Ko-odinetantan Shirin Zamanantar da Kiwo da Bunƙasa Sana’ar Dabbobi (L-PRES), Farfesa Usman Bello Abubakar da kuma Babban Daraktan sashin bincike da tattara bayanai, Ahmed Hussaini.

Manajan Bunƙasa Kiwo na Duniya Jason Schrier, da Babban Masanin Kimiyya Dakta Lorna McNaughton ne suka wakilci Cibiyar ta LIC.

An kafa Cibiyar ta Bunƙasa Kiwon Dabbobi ne a shekarar 1909, kuma tana kan gaba a fannin fasahar noma da inganta kiwon dabbobi a duniya, tana tallafawa masu kiwo a duk duniya ta hanyar amfani da fasahar zamani, da manhajar kula da garaken shanu, da kuma bada shawarwari na musamman

Kimiya, Labarai, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Kasar Colombia Tare Da Amurka Zasu Fitar Da Man Venezuela
Next Post: An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure

Karin Labarai Masu Alaka

Masu Goyon Bayan Palasdinawa Sunyi Gangamin Zanga Zanga A Australia Labarai
Soyinka Ya soki Yawan Jami’an Tsaron Da Ake Bai Wa Seyi Tinubu Najeriya
Amurka Da Kasashen Yamma Suna Cigaba Da Kai Ruwa Rana Akan Nukiliyar Iran Afrika
Rundunar Hadinkan Saudiya Tayi Ikirarin Mayar Da Martani Ga ‘Yan Aware Labarai
Kamfanin Dangote Zai Sayo Na’urori Daga Kasar China Kimiya
Majalisar Dinkin Duniya Ta Amince Da Kudurin Kasar Ghana Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kungiyar Cigaban Al’ummar Tangale Tace Bata Goyon Bayan Kai Ziyara Wa Gwamnan Gombe Labarai
  • Shugaba Trump Yace Tehran Tana Neman Kulla Alaka Da Washington Amurka
  • Margayi Shugaba Muhammadu Buhari 1942-2025 Labarai
  • Amurka Ta Daina Bawa Israila Bayanan Sirri Amurka
  • Zulum Ya Rushe Majalisar Zartarwa Ta Jihar Borno Afrika
  • Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Ya Sauka A Mukaminsa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mutane Biyu Sun Mutu A Yayin Zaben Shugabannin Gundumomin APC A Jihar Ondo Najeriya
  • EFCC Ta Cafke Fitacciyar Jarumar Kannywood Samha Inuwa Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.