Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Gwamnatin Najeriya Ta Taya Super Eagles Murnar Lashe Tagulla A Gasar AFCON
Published: January 18, 2026 at 10:12 AM | By: Bala Hassan | Updated: January 18, 2026

Gwamnatin Tarayya ta taya Super Eagles murna bisa samun lambar tagulla a gasar AFCON.

Gwamnatin Tarayya ta taya ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles murna bisa samun lambar yabo ta tagulla a gasar Kofin Nahiyar Afrika (AFCON) ta 2025, inda ta bayyana rawar da ƙungiyar ta taka a matsayin abin alfahari da farin ciki ga ’yan Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya jinjina wa ‘yan ƙungiyar bisa yadda suka ɗaukaka tarihin ƙwallon ƙafa na Nijeriya da zuciya ɗaya, ƙwarewa, da jajircewa a tsawon gasar.

A cewar Ministan, Super Eagles sun nuna jarumta, haɗin kai, da amincewa da juna tun daga matakin rukunoni har zuwa busar ƙarshe a birnin Kasablanca na ƙasar Marokko, wanda hakan ya zaburar da miliyoyin ‘yan Nijeriya a gida da kuma ƙasashen waje.

Ya bayyana cewa irin wasan da suka yi ya wuce kawai buga ƙwallo, domin ya farfaɗo da kishin ƙasa da kuma kyakkyawar fata.

Ministan ya ce samun lambar tagulla ya sake ƙara wa tarihin nasarorin Nijeriya armashi a gasar AFCON, tare da ƙarfafa martabar da Super Eagles ke da ita a nahiyar.

Ya yaba wa ladabi da ruhin gwagwarmaya na ƙungiyar, musamman a wasannin da suka fafata da gaggan ƙungiyoyi.

Haka kuma, ya miƙa godiyar sa ga masu horaswa, ma’aikatan tallafi, da ‘yan wasan bisa sadaukarwa da jajircewar su duk da ƙalubalen da suka fuskanta.

Ya jaddada cewa wasan nasu ya nuna muhimmancin aiki tare, imani, da alfahari wajen wakiltar Nijeriya, ya ƙara da cewa wannan ƙoƙari ya sake tabbatar da matsayin Nijeriya a matsayin babbar ƙasa a ƙwallon ƙafar Afrika.

Ko da yake ya bayyana cewa babban kofin ta suɓuce musu a wannan karo, Ministan ya jaddada cewa an samu lambar tagullar cikin mutunci da ƙoƙari, kuma ba ta ‘yan wasan ba ce kawai, har ma ta ɗaukacin ‘yan Nijeriya ce waɗanda suka ba su goyon baya kuma suka yi imani da su a duk tsawon gasar.

Ya buƙaci Super Eagles da su yi murnar wannan nasara cikin alfahari, tare da ɗaukar ta a matsayin abin ƙarfafa gwiwa domin tunkarar duk wani ƙalubale nan gaba, sannan ya nuna godiya da jinjina kan yadda suka wakilci ƙasar nan.

Wasanni

Post navigation

Previous Post: FRSC Gombe: Hatsarin Mota Ya Yayi Ajalin Mutane 38 Ya Jikkata Fiye Da 218 A Wata Ɗaya
Next Post: ADC Ta Sha Damarar Gwabzawa Da APC A Zaben 2027

Karin Labarai Masu Alaka

An Dakatar Da Daniel Bisa Zargin Fyade Wasanni
CAF Ta Fara Binciken Rikicin Bayan Wasa Tsakanin Algeria Da Najeriya Wasanni
Da Alamu Ronaldo Zai Buga Dukkan Wasanni Da Gasar Kofin Duniya A 2026 Wasanni
CAF, Zata Ci Tarar Wasu Kasashe AFCON 2025 Wasanni
FIFA, Ta Raba Jaddawalin Rukuni Na Gasar Kofin Duniya 2026. Wasanni
Kocin Ranchers Bees Ya Yi Murabus Wasanni

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Bahagon Mancha Ya Buge Bahagon Maitakwasara Da Wasun Su! Nishadi
  • Anyi Asarar Biliyoyin Naira A Gobarar Kasuwar Singa Labarai
  • Kano Pillars Ta Doke Ikorodu City Wasanni
  • FIFA Na Shirin Fadada Babban Na’urar VAR A Gasar Cin Kofin Duniya 2026. Wasanni
  • Ranar Talata Amurka Da Isra’ila Sun Cigaban Da Kai Farmaki Iran Afrika
  • Mataimakin Shugaban Kasa Ya Sauka A Jihar Kwara Labarai
  • Sakataren Tsaron Amurka Yace Baza’a Bayyana Bidiyon Kai Hari Akan Jirgin Ruwa Ba Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.