Za a dinga yin gwajin shan miyagun ƙwayoyi ga ma’aikata kafin a dauke su aiki inji Gwamnatin tarayyae Najeriya
Gwamnatin taayya ta ta sanar da shigo da tsarin gwajin miyagun ƙwayoyi na dole a matsayin sabon sharadi kafin daukar aikin gwamnati.
An fitar da wannan umarni ne ga manyan sakatarorin ma’aikatu da shugabannin hukumomi a wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin.
Daraktan yada labarai da hulɗa da jama’a a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF), Segun Imohiosen, ya bayyana cewa sabbin sharuɗɗan na daga cikin kokarin gwamnati na dakile karuwar amfani da haramtattun ƙwayoyi da illolinsu ga ci gaban ƙasa da tsaro.
Ya kara da cewa an dauki matakin ne sakamakon damuwar da gwamnati ke da ita kan yawaitar shan miyagun ƙwayoyi da sauran kwayoyi masu sa maye, musamman a tsakanin matasa.
A cewarsa, wannan “mummunan yanayi” na da manyan illoli ga lafiyar jama’a, ci gaban zamantakewa da tattalin arziki, ingancin aiki a wuraren aiki, da kuma tsaron ƙasa.
An umurci ma’aikatu, sassa da hukumomi da su yi aiki tare da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) wajen gudanar da gwaje-gwajen, bisa ka’idoji da tsare-tsaren da aka amince da su.


