Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Gwamnatin Tinubu Ta Karyata Kafa Kamfanin Gwal A Legas
Published: January 20, 2026 at 11:25 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ma’aikatar albarkatun ma’adinai ta musanta zargin da kungiyar dattan Arewa (NEF) ta yi cewa gwamnatin tarayya ta kafa masana’antar sarrafa gwal a Legas tare da karya ƙa’idar daidaiton tarayya.

A wata sanarwa da Segun Tomori, mataimaki na musamman kan yaɗa labarai ga ministan albarkatun ma’adinai, Dele Alake, ya fitar, ya bayyana cewa masana’antar da ake magana a kai ba ta gwamnati ba ce, illa dai aikin kamfanin Kian Smith mai zaman kansa.

Tomori ya ce babu inda ministan ya taɓa bayyana cewa gwamnati ce ta mallaki ko ta kafa masana’antar gwal a Legas, yana mai ƙara da cewa dukkan masana’antun gwal da ake shirin ƙaddamarwa a sassan ƙasar mallakar kamfanoni masu zaman kansu ne.

Ya bayyana cewa masana’antar ta zo ne sakamakon manufar ƙara darajar albarkatu da ma’aikatar ta ƙaddamar shekaru biyu da suka gabata, wadda ke ƙarfafa sarrafa ma’adinai a cikin gida maimakon fitar da su danye.

Tomori ya kuma soki NEF bisa abin da ya kira rashin yin bincike kafin fitar da zargi, yana mai cewa ba zai yiwu a tilasta wa kamfani mai zaman kansa ya kafa aikinsa a wani yanki na musamman ba.

A ƙarshe, ya buƙaci NEF da ta goyi bayan ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da ƙarfafa dogaro da kai.

Labarai, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Fadar Sarkin Musulmi: Talata Ne 1 Ga Watan Sha’aban Na 1447AH
Next Post: CBN: An Samu Ƙaruwar Masu Cin Bashin Banki Basa Biya

Karin Labarai Masu Alaka

Amurka Ta Kulla Yarjejeniya Da Kasashe Hudu Domin Inganta Kiwon Lafiya Labarai
Kotu A Kasar Tunisiya Ta Daure Wani Babban Dan Kasuwa Da Wasu ‘Yan Majalisa Afrika
Hukumar Tsaron Civil Defence A Gombe Ta Samar Da Jami’ai Don Tabbatar Da Tsaro A Bukukuwan Karshen Shekara Labarai
Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki Labarai
Jirgin Sama Mai Saukar Ungulu Ya Kashe Mutane Biyar A Tanzaniya Afrika
Shugaba Trump Ya Bukaci A Cigaba Da Zanga Zanga A Iran Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Onana Ba Ya Cikin Tawagar Kamaru (AFCON) Wasanni
  • Jihar Kano Tayi Rashin ‘Yan Majalisu Biyu Najeriya
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Fiye Da Mutane 50 Tare Da Sace Mata Da Yara A Jihar Zamfara Najeriya
  • Ingila, Hauhawar Farashi Yayi ƙasa Sosai Labarai
  • Wasu Zakaru Da Suka Samu Karramawar Hukumar CAF Ta Afrika Wasanni
  • Chadi Ta Sauyawa ‘Yan Gudun Hijira Matsuguni Afrika
  • An Gudanar Da Zanga-Zanga A Kasar Somaliya Labarai
  • Babangida: Hakika Abiola Ya Lashe Zaben Watan Yuni 1993 Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.