Mummunan hatsari yayi Ajalin Mutane bakwai a jihar Gombe, yayinda Gwamna Inuwa Yahaya Ya Miƙa Ta’aziyya Ga Al’ummar Lawanti Sakamakon Wannan Hatsari
Rahotanni sun ce waɗanda abin ya shafa suna kan hanyarsu ta zuwa Maiduguri babban birnin jihar Borno, don halartar wani bikin aure.
An bayyana sunayen mamatan kamar haka, Gambo Abbo, mai shekara 35, Umalkhairi, mai shekara 18, Rabiu Abubakar, mai shekara 28, Fatuma Hassan, mai shekara 28, Amal Abubakar, mai shekara 3 Adamu Bello, mai shekara 4 da Zarau Alhaji, mai shekara 27.
Da yake tsokaci kan wannan mummunan labari, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi mai raɗaɗi da ban tsoro, ba kawai ga iyalan da abin ya shafa ba, har ma ga dukkan al’ummar Lawanti, Ƙaramar Hukumar Akko da kuma jihar Gombe baki ɗaya.
Yace mutuwar kwatsam ta irin waɗannan mutane masu tasiri ta taɓa zuƙatan kowa, yana mai cewa babu wata kalma da za ta iya ta’azantar da iyalan waɗanda suka rasa ƙaunatattunsu a cikin irin wannan yanayi mai ban tausayi.
Gwamnan ya jajantawa iyalan waɗanda abin ya shafa, musamman Hakimin Jalingo, Bello Hassan Babangida wanda ya rasa ‘yar uwarsa da kuma yayansa da Idris Lawanti Maigari, wanda ya rasa ‘yarsa da Kansila mai wakiltar Gundumar Akko, Idris A. Isah Lawanti, wanda shi ma ya rasa ‘yan uwa na kurkusa.
Ya yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki ya baiwa iyalan da suka rasu, da ƴan uwa da kuma duk al’ummar Lawanti yayi fatan su zamo masu juriya, haƙuri da ƙarfin halin ɗaukar wannan babban rashi, sannan kuma Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu da rahamarsa.
Gwamna Inuwa Yahaya ya kuma yi addu’ar Allah ya gafartawa mamatan abyafe kurakuransu, ya karɓi kyawawan ayyukansu ya kuma saka musu da Aljannatul Firdausi.


