Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya wato (NDLEA), ta kama wata mata da miyagun ƙwayoyi a cikin juna biyu na bogi a iyakar ƙasa ta Seme Border da ke Legas.

An cafke ‘yar kasuwar ‘yar asalin Kano mai suna Rabi Muhammad, mai shekara 35, a ranar Litinin 16 ga Fabrairu, 2026, a harabar tashi ta kan iyakar Seme ya yin da take ƙoƙarin tsallakawa zuwa Cotonou a ƙasar Benin.


