A halin da ake ciki, ka’idoji guda 10 da Iran ta gabatar na kawo karshebn yaki a tsakaninta da Amurka da Iran, sun biyo bayan wasu ka’idojin ne guda 15 da Amurka ta gabatar mata ta hannun Pakistan da nufin kawo karshen yakin.
Sharrudan na Amurka sun hada da tsagaita wuta nan take, da sake bude mashigin ruwan Hormuz, da tattaunawar yin sulhu cikin kwanaki 15 zuwa 20 da kuma wasu ka’idoji da yaka shafi rawar da Ukraine ran ke takawa a yankin da kuma take-taken sojojinta.
Iran ta yi watsi da su tana mai fadin cewa tsagaita wuta ba zai haifar da komai ba, idan bawai an kawo karshen yakin ba ne baki dayansa.
Kamar yadda jaridar Wall Street Journal ta wallafa, sharruda guda 10 da Iran ta gabatar na tsagaita wuta da kawo karshen yakin sune, Amurka ta tabbatar mata a rubuce cewar ba zata sake kai mata farmaki ba, da ci gaba da rike ikon mashigin ruwan Hormuz; da amincewa da ikon kasar Iran na I gaba da tace makamashin Uranium domin amfanin shirinta na nukiliya; da kawar da duk wani takunkumin da aka saba ma kasar, da kawar da duk wani takunkumin da aka sanya a kan wasu cibiyoyin Kasashen waje masu huldar cinikayya da Iran, da kawo karshen duk wani kudurin kwamitin Sulhu MDD da aka yi kan Iran, da kawo karshen duk wani kudurin da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta yi kan Iran, da biyan Iran diyyar abubuwan da aka lalata mata a yaki, da janye sojojin Amurka daga yankin Gulf; da kuma tsagaita wuta a dukkan inda ake fada ciki har da farmakin da Isra’ila ta kai kan ‘yan hezbollah a Lebanion.


