Ahalinda ake ciki kuma, Iran ta kama mutane da dama ciki har da wani dan kasar ketare kan zargin suna yi wa “makiyan” kasar leken asiri, kamar yadda ma’aikatar tsaron kasar ta fada ranar talata, a dai dai lokacin da ake ci gaba da yakin hadin guiwar da Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan kasar.
Ba tare da ta ambaci kasar da wadanda aka kaman suka fito ba, ma’aikatar tsaron Iran tace dan kasar ketaren “yana yi wa Amurka da Isra’ila leken asiri, kuma dan koren wasu kasashe biyu da suke yankin Gulf, kamar yadda wata kafar yada labaran kasar ta fada.
A shekarun baya bayan nan, rundunar juyin juya hali ta Iran ta kama gomman mutane wadanda asalin su ‘yan Iran ne masu ruwa biyu, kan zargin leken asiri da kuma harkar tsaro.
A ranar 28 ga watan Febwairu ne Amurka da Isra’ila suka kaddamar hare hare kan Iran har suka kashe shugaban addinin kasar Ayatollah Ali Khameni, da wasu kwamandajin kasar.


