Iran na duba wata shawara daga Amurka da ke da nufin kawo ƙarshen yaƙin da ke gudana a yankin Tekun Gulf, amma ba ta da niyyar shiga tattaunawa domin dakatar da rikicin Gabas ta Tsakiya da ke ƙara faɗaɗa, in ji ministan harkokin wajen ƙasar a jiya Laraba.
Kalaman Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, sun nuna cewa, Tehran na da wani ƙaramin shiri na shiga tattaunawa don kawo ƙarshen yaƙin, matuƙar an biya buƙatun ta.
Sai dai ya jaddada cewa, musayar saƙonni ta hannun masu shiga tsakani “ba yana nufin ana tattaunawa kai tsaye da Amurka ba,” kamar yadda ya bayyana a gidan talabijin na ƙasa.
Ya ƙara da cewa: “Sun gabatar da wasu shawarwari a cikin saƙonninsu waɗanda aka miƙa wa manyan shugabanni, kuma idan ya zama dole, za su fitar da matsayinsu.”
Shirin na shugaban Amurka Donald Trump da aka kira 15-point Agenda, kudurori 15, wadda aka aika ta hannun Pakistan, ya bukaci Iran ta daina ajiye sinadarin uranium mai ƙarfin gaske, ta dakatar da aikin sarrafa uranium din, da kuma takaita shirin makamai masu linzami na ballistic, da kuma dakatar da tallafin kuɗi ga ƙawayenta a yankin, a cewar wasu majiyoyi uku daga majalisar ministocin Isra’ila da suka san da wannan shiri.


