Fushin jama’a akan Washington ba shi da yawa a duk faɗin ƙasashen Gulf, duk da cewa sun fuskanci tashin hankali mafi muni, sun bukaci Amurka da ta dakatar da fadan.
Ban da wasu, manyan jami’an yankin Gulf sun nisanta kansu daga zargin Washington a bainar jama’a kan matakin da ta dauka na tunkarar Iran. Manyan kasashen yankin Gulf suna Kallon Iran a matsayin maciyiyar amana, ba ga Amurka ba, duk kuwa da cewar matakin Amurka ya taimaka wajen ruruta rikici.
Wani hamshakin mai kudi Khalaf Al Habtoor wanda yayi wasu kalamai da ba’a saba gani ko ji ba, ya kalubalanci Donald Trump a takaice kan “jawo” yankin cikin yaki, amma daga bisani ya janye kalaman wannan wata alama ce, da ke nuni da cewar yankin na Gulf yana cikin rashin kwanciyar hankali da nuna Rashin jin dadin su da Washington.
Shugaban Kamfanin Aramco Amin Nasser ya kauracewa yin suka ga Washington, duk da cewa ya yi gargadin cewa yakin zai haifar da “mummunan yanayi” tare da yiwuwar “mummunan bala’i” ga kasuwannin mai na duniya.


