Ƙasar Nijar, maƙwabciyar Najeriya a Arewa, ta fitar da wata doka ta musamman kan tura ‘yan ƙasa aikin kare ƙasa, biyo bayan harin haɗin gwiwa da Najeriya da Amurka suka kai kan sansanonin ‘yan ta’adda a jihar Sokoto a daren ranar Alhamis.
Cikin kasa da sa’o’i 24 bayan hare-haren sama, Majalisar Ministocin Nijar ta gudanar da taro a birnin Niamey ƙarƙashin jagorancin Janar Abdurahamane Tiani, inda ta amince da kudirin wata doka da ke neman ‘yan Nijar su shiga cikakken shirin tura jama’a domin kare ƙasar.
Karamar Hukumar Tangaza, wadda ita ce babbar manufa ta harin makaman Tomahawk, tana kan iyakar da ke tsakanin Najeriya da Nijar.
Jami’an Najeriya da na Amurka sun ce ayyukan yaƙi da ‘yan ta’adda a Arewa na ci gaba da gudana.
Haka kuma, Amurka ta riga ta cigaba da gudanar da ayyukan tattara bayanan sirri da sa ido a dajin Sambisa da ke jihar Borno, bayan hare-haren makamai masu linzami da aka kai a Sokoto.
A ƙarƙashin dokar Nijar, an umarci ‘yan ƙasa da su amsa kiran gwamnati nan take, su bi duk umarnin kwace kayan aiki, su kai rahoton baki ko baƙin ‘yan ƙasa masu haɗari ko ayyukan da ka iya hana shirin tura jama’a aiki, tare da gujewa yada bayanai ko saƙonni da za su iya raunana wannan shiri.


