Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Jihar Borno Ce Tayi Nasara A Gasan Karatun Al Qur’ani Na Kasa
Published: December 20, 2025 at 12:44 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya ce ta lashe matsayi na ɗaya a rukunin maza a Gasar Karatun Al-Qur’ani ta Ƙasa ta shekarar 2025, wadda aka gudanar a Maiduguri ƙarƙashin taken “Borno 2025.”

Wannan gasa ta zama abin tarihi, domin ita ce karo na 40 da ake gudanarwa a Najeriya kuma Borno ta yi nasarar karɓar baƙuncinta cikin nasara.

Yayin sanar da sakamakon gasar, Daraktan Cibiyar Nazarin addinin Musulunci ta Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Abubakar Yelwa, ya bayyana Musa Ahmed Musa daga jihar Borno a matsayin zakaran a rukunin maza.

A rukunin mata kuma, Hafsat Muhammad Sada daga Jihar Kano ce ta zama Dawisu.

Gasar wadda ta ɗauki tsawon mako guda, ta samu mahalarta mutane 296 daga jihohi 30 na Najeriya, inda suka fafata a rukunai daban daban.

Da yake jawabi a bikin rufe gasar, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana nasarar gudanar da gasar a matsayin alamar dawowar zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Borno.

Ya ce gasar ta nuna jajircewar al’ummar jihar wajen zaman lafiya, ilimi da koyarwar Musulunci.

“Nasarar ku ba kawai cin gasa ba ce,” in ji Gwamna Zulum ga waɗanda suka yi nasara, “amma wata babbar nasara ce da ta samo asali daga dogon lokaci na jajircewa, himma da girmama Kalmar Allah.”

Ya kuma yaba wa dukkan mahalarta gasar, inda ya ce, “Hakikanin ruhin wannan gasa ba wai lambobin yabo kawai ba ne, amma neman ilimi da jarumtar shiga gasar.”

Gwamnan ya nuna godiya ga Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, da matarsa Hajiya Nana Kashim Shettima, da sauran manyan baƙi da suka bayar da gudunmawa wajen samun nasarar gasar.

Haka kuma, ya yaba da rawar da sarakunan gargajiya, shugabannin jami’o’i, malaman addinai da shugabannin siyasa suka taka wajen nasarar taron.

Manyan baƙi da suka halarci taron sun haɗa da matar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Hajiya Nana Kashim Shettima, Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Dikko Umar Radda, Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato, Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi, ‘yan Majalisun Tarayya da jihohi da malaman addini.

Babban abin da ya kayatar a bikin shi ne rabon kyaututtuka da lambobin yabo ga waɗanda suka yi nasara, wanda matar Mataimakin Shugaban Ƙasa ta gabatar.

Najeriya

Post navigation

Previous Post: Tinubu Ya Buƙaci Gwamnoni Su Mutunta Hukuncin Kotun Ƙoli Kan ’Yancin Kuɗin ƙananan Hukumomi
Next Post: Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Zuwa Jami’ar Sheikh Dahiru Bauchi

Karin Labarai Masu Alaka

Haryanzu Abubakar Malami Da Dansa Suna Hannun Hukumar EFCC Labarai
Motar Kungiyar Kwallon Kafar Bayelsa United Ta Yi Hatsari Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Amurka Zata Hana Kwankwaso Shiga Kasar Amurka
Rundunar ‘Yan Sanda Sun Ceto Wani Daga Hannun Masu Garkuwa Najeriya
Shugaba Bola Tinubu Ya Saka Hannu A Dokar Zabe Najeriya
Sanatan Nasarawa Ta Arewa Ya Rasu A Kasar India Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Amurka Zata Saidawa Saudiyya Da Jirgin Yaki Samfurin F35 Labarai
  • Wasu Zakaru Da Suka Samu Karramawar Hukumar CAF Ta Afrika Wasanni
  • Shugaba Tinubu Ya Umurci Janyewa Manyan Mutane ‘Yan Sanda Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Kasashen Afirka Da Dama Suna Fafatawa Da Rasha A Yaki Da Ukraine Afrika
  • ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane A Kauyuka Dake Yammacin A Najeriya Najeriya
  • Afirka Ta Kudu Zata Fuskanci Koma Baya A Bangaren Samar Da Ayyukanyi Afrika
  • An Kaddamar Da Rijistar Zamani Ta Zamowa Mamba A Jam’iyar APC Siyasa
  • Emmanuel Macron: Yakamata Wani Sashi Ya Rika Takawa Wani Sashi Birki A Tsarin Demokradiya Amurka Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.