China da Amurka da wasu kasashen daga yammacin duniya sun hada kai na ba safai ba domin matsawa Ghana lamba ta rage karin kudin haraji kan masu hakar zinari da take kudurin dauka da suke ganin zai iya yin rauni ga manyan kamfanonin hakar zinari a duniya, kamar yadda wasu majiyoyi uku da wata wasika daga wata Kungiyar masu hakar ma’adinai suka bayyana.
Ghana wacce itace kasar da ta fi kowacce a duniya hakar zinari tana shirin sauya kudin haraji kan hakar zinari daga kashi biyar cikin dari, da wani sabon tsari da zai tashi kuma ya sauka, daga kashi biyar zuwa kashi 12 cikin dari, da nufin samawa gwamnati karin kudaden shiga ganin yadda kasuwar zinari ko gold ya tashi zuwa matsayi da ba’a taba ganin haka ba.
Kodashike kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bada rahoton Ghana ta yi niyyar rage kudin haraji domin ya sami amincewa kan sabuwar dokar da zata fara aiki makon gobe, duk da haka masu hakar ma’adinai suka ce idan har dokar ta tabbata zata sa Ghana ta kasance wacce ta fi ko wace kasar Afirka tsadar hakar ma’adinai, kuma hakan zai shafi ribar su sosai.
Baya ga matsin lamba Amurka da China, ofisoshin jakadancin Ingila, da Canada, da Australia da Afirka ta kudu, duk sun tsoma baki kan wannan kuduri, wadda wasu manyan jami’an kamfanonin hakar ma’adinai su uku suka ce kasashen sun nuna wani hadin kai na ba safai ba domin tunkarar wata dokar haraji.


