Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Koriya Ta Arewa Ta Gudanar Da Gwajin Makami Mai Linzami
Published: January 5, 2026 at 5:35 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Kamfanin dillancin labaran Koriya ta Arewa, ya ba da rahoton cewa ranar lahadi, kasar ta gudanar da gwajin harba makamai masu linzami masu tsananin gudu, a wani matakin auna irin karfin sojojinta da makamansu na kare kai.

Shugaba Kim Jong Un, wanda ya sanya idanu wajen harba makaman, yace mataki ne mai matukar muhimmanci ga kasar ta ci gaba da kasancewa tana da karfin makaman nukiliya, ko ta fadada su, domin zamowa hannunka mai sanda ga duk mai neman kai mata farmaki.

Kamfanin dillancin labaran na KCNA yace makaman sun fada kan inda aka auna su kimanin kilomita dubu daya a tekun dake gabas da Koriya ta Arewa.

A ranar lahadi, rundunar sojojin Koriya ta Kudu, ta ce Arewa ta harba makamai masu linzami a tekun dake gabas da kasar a daidai lokacin da shugaban Koriya ta Kudu, Lee Jae Myung ya fara ziyarar aiki a kasar China.

Harba wadannan makamai masu linzami masu tsananin gudu da Koriya ta Arewa ta yi, ya biyo bayan fitowar da ta yi tana yin Allah wadarai da harin da Amurka ta kai a kan Venezuela a zaman wanda ya keta haddin diyaucin kasar.

Tsaro

Post navigation

Previous Post: Shugaba Trump Yace Amurka Ce Zata Rika Gudanar Da Harkokin Kasar Venezuela
Next Post: Kasar Botswana Na Samun Kudaden Shiga Da Lu’ulu’u

Karin Labarai Masu Alaka

Meyasa Israela Take Hana Kaiwa Gaza Kayan Tallafi Afrika
‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 30 A Jihar Neja Najeriya
Kasar Chadi Ta Rufe Iyakar Ta Da Kasar Sudan Afrika
Rundunar ‘Yan Sanda Sun Ceto Wani Daga Hannun Masu Garkuwa Najeriya
Sojojin Amurka Sun Isa Najeriya Don Yaki Da Ta’addanci Amurka
Tarayyar Turai Zasu Kirkiro Sojojin Haɗin Gwiwa Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Amurka Da Iran Zasu Tattauna A Kasar Oman Amurka
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Gabatar Da Kudi Fiye Da Naira Triliyan 58 A Matsayin Kasafin 2026 Najeriya
  • Babangida: Hakika Abiola Ya Lashe Zaben Watan Yuni 1993 Labarai
  • Shugaba Saied Yana Cigaba Da Samun Goyon Bayan Al’ummar Kasar Tunisiya Afrika
  • Anfara Kirga Kuri’a A zaben Kasar Guinea Labarai
  • Yau Litinin Ake Cigaba Da Shari’ar Najib Zarak Labarai
  • Sabon Jadawalin Gasar Kwalon Kafa Ta Turai 2026 Wasanni
  • Cutar Kurkunu Ta Kusa Zamowa Tarihi A Duniya Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.