Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Kotun Uganda Tayi Watsi Da Karar Hukumomin Kasar
Published: February 3, 2026 at 10:09 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Wata kotu a Uganda ranar Litinin, tayi watsi da karar da hukumomin kasar suka shigar kan mutum na farko da ake tuhuma da laifin “luwadi mafi tsanani,” laifi da idan kotu ta tabbatar ana yanke masa hukuncin kisa, kamar yadda lauyan mutumin ya gayawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Dokar wacce Uganda ta kafa a shekarar 2023, inda tayi kunnen kashi daga matsin lambar kasashen yammacin duniya, da kungiyoyin kare hakkin Bil’adama na gida da ketare, ana kallon dokar a zaman mafi tsanani a duniya kan ‘yan luwadi, dokar ta yi tanadin daurin rai da rai idan aka kama mutum da laifin luwadi, sannnan ta tanadi hukuncin kisa bisa wasu dalilai na musamman. Sharuddan sun hada da maimaita laifin da ake zargin mutum dashi, ko yin luwadi ga mutumin da bai balaga ba, ko ga tsoho, ko mutumin da yake dauke da wata larura.

Wanda ake tuhuman a yanzu dan shekaru 20 da haifuwa, an kama shi ne a shekara ta 2023, kan zargin yayi luwadi da wani mutum dan shekara 41 da haifuwa, wadda ya fada karkashin rukunin laifi na musamman, kamar yadda lauyansa ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Reuters ranar talata.

Ranar Litinin, Alkali a kotun majistrate a Uganda, ya kori karar, bayanda kotu ta fahimci cewa mutumin ya sami gushewar hankali, saboda tsawon lokaci da yayi yana tsare.

Kakakin kotunan Uganda bashi da ta cewa da aka tuntube shi kan wannan shari’ar.

Afrika, Labarai

Post navigation

Previous Post: Bincike Yanuna Kasashen Afirka Suna Cikin Mafiya Cin Bashi A Duniya
Next Post: Wakilan Majalisar Dokokin Phillipines Suna Yunkurin Tsige Shugaban Kasar

Karin Labarai Masu Alaka

Jirgin Dakon Iskar Gas Daga Rasha Ya Sake Hanya Afrika
Gwamnatin Kasar Ghana Ta Rage Farashin Cocoa Afrika
Jama’a A Yankin Gulf Sun Bukaci Dakatar Da Hare Hare Daga Washington Afrika
Yakin Iran Da Isra’ila Da Amurka Zai Shafi Kasashen Afirka – Masana Afrika
Shugaba Tinubu Ya Gana Da Takwaransa Na Kasar Jamus Akan Sha’anin Tsaro Labarai
An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kwankwaso: Gwamnatin Kano Tamuce Baki Daya, Tafiya APC Allah Ya Raka Taki Gona! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Sarkin Kagarko Ya Rasu Yana Da Shekaru 110 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Tsananin Sanyi Ya Kashe Mutane 38 A Amurka Amurka
  • Wasan Dambe Ya Dau Sabon Salo A Jihar Inugu Wasanni
  • Jam’iyar NNPP: Abba Kabir Yusuf Yaci Amanar Mu Siyasa
  • An Farmaki ‘Yan Bindiga Da Dama A Jihar Zamfara Labarai
  • Harin Iran A Kasar Saudiya Ya Haifar Da Tattaunawa Tsakanin Shugabanni Afrika
  • Amurka Tana Cigaba Da Kare Jami’in Da Ya Kashe Ba Amurke Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.