Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CDEAO, ta bayyana rashi yardarta da shirin mayar da mulki hannun farar hula da shugabannin mulkin soja na Guinea-Bissau, suka bayyana, tana mai bukatar da a gaggauta maido da aiki da tsarin mulki.
Shugabannin ECOWAS, sun yi barazanar saka takunkumi na musamman a kan duk wadanda ke kawo cikas ga maido da mulkin farar hula a kasar.
A ranar 26 ga watan Nuwamba ne wasu hafsoshin soja a Guinea-Bissau suka hambarar da shugaba Umaro Sissoco Embalo, kwana daya kafin a bayyana sakamakon zaben shugaban kasa, kashegari kuma suka ayyana Manjo Janar Horta Inta-a a matsayin shugaban gwamnatin mulkin soja na wuin gadi.
Wannan juyin mulki da aka yi a Gyuinea-Bissau, shine na tara cikin shekaru 5 da suka shige a yankin yammaci da tsakiyar Afirka, abinda ya kara irin fargabar da ake yi ta zaizayewar mulkin dimokuradiyya a wannan yanki mai fama da rashin tsaro da rashin kwanciyar hankalin siyasa.
Shugabannin dake halartar taron kolin shekara na kungiyar ECOWAS ranar lahadi a Abuja, babban birnin Najeriya, sun yi kiran da a sako dukkan ‘yan siyasar da aka kama, ciki har da shugabannin hamayya, a kuma tsara shirin maida mulki cikin gaggawa wanda zai kumshi dukkan sassan kasar cikin gaggawa.
Shugaban majalisar zartasa ta kungiyar ECOWAS, Omar Touray, yace matakin da shugabannin kungiyar suka dauka shine na tabbatar da cewa sam ba za a taba yarda da sauya gwamnati ta hanyar da tsarin mulki bai amince ba.
ECOWAS ta ce ‘yan kallonta, da na Kungiyar Tarayyar Afirka da na kasashe masu magana da harshen Portugal duk sun ce zaben shugaban kasa da aka gudanar a Guinea-Bissau, an yi shi cikin adalci.
Har ila yau kungiyar ta umurci shugabanta da ya jagoranci wata tawaga ta manyan jami’ai zuwa Gyuinea-Bissau domin tattaunawa da hukumomin sojan kasar.


