Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Kungiyar ‘Yan Ta’adda Masu Alaka Da ISIS Sun Kashe Mutane A Congo
Published: January 26, 2026 at 8:50 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Wasu ‘yan kungiyar ‘yan ta’adda da ke da alaka da kungiyar ISIS a gabashin Congo sun hallaka a kalla mutane 25 a cewar masu rajin kare hakki a lardin Ituri.

Wadanda aka kashe sakamakon harin da kungiyar Allied Democratic Forces, wato IDF ta kai, sun hada da maza 15 da aka kone da ran su a wani gida, da wasu 7 da aka harbe a kauyen Apakulu, a yankin Irumu da ke lardin Ituri. Uku kuma an kashe su ne a yankin gudanar da ayyuka na Walese Vonkutu.

Shugaban kungiyar masu rajin kare hakki, Christophe Muyanderu, yace abun ya faru wajajen karfe 4 na asuba, inda rayuka a kalla 25 suka salwanta. Ya kara da cewa wannan hari na ADF kisan gilla ne karara.

Ba’a ji daga kungiyar ta ADF kan lamarin ba.

Jamhuriyar Demokradiyar Congo dai na yawan samun hare-hare a watannin baya bayan nan daga kungiyoyin ‘yan tawaye da suka hada da ADF kuma kungiyar M23 da kasar Rwanda ke marawa baya.

Tsaro

Post navigation

Previous Post: Za’a Gurfanar Da Sojojin Da Ake Zargi Da Yunkurin Juyin Mulki
Next Post: Sojojin Faransa Sun Karyata Zargin Bobi Wine

Karin Labarai Masu Alaka

Ankara Gano Wani Abu Mai Kama Da Abun Fashewa A Jabo Jihar Sokoto Tsaro
Farashin Mai Yana Cigaba Da Karuwa Afrika
Rundunar Sojin Najeriya Ta Dakile Harin ‘Yan Ta’adda A Jihar Borno Labarai
Wasu Mayakan ‘Yan Tawaye Sunkai Hari Filin Jirgin Saman Kasar Kwango Labarai
Iran Ta Tsagaita Kai Hare Hare Makwabta Afrika
Hukumar ‘Yan Sanda Ta Dawo Da Dokar Zirga Zirgar Babura A Jihar Gombe Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Fiye Da Mutane 15 A Kasar Australiya Labarai
  • Ministan Yaɗa Labarai: Ceto Daliban Neja An Samu Natsuwa A Kasa Labarai
  • Amurka Da Tarayyar Turai Sun Fidda Sanarwa Afrika
  • Jihar Kano Tayi Rashin ‘Yan Majalisu Biyu Najeriya
  • An Kafa Majalisar Kotun Sulhu Ta Kano Labarai
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki Labarai
  • Kasashe Biyar Zasu Tura Sojoji Domin Ayyukan Wanzar Da Zaman Lafiya A Gaza Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Laraba 11.19.2025 Rediyo
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.